Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Tinubu Ya Jaddada Buƙatar Kare Rayukan ‘Yan Afirka A Taron ECOWAS
Published: July 21, 2026 at 10:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da ta ɗauki tsauraran matakai kan ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka a ƙasar Afirka ta Kudu.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yayin taron shugabannin ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a birnin Freetown na ƙasar Saliyo.

Ya ce ya zama dole ECOWAS ta gabatar da batun a gaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), domin a ɗauki matakin gaggawa kan hare-haren da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin ‘yan Afirka.

Shugaban ya ce gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da hare-haren, tana mai bayyana cewa ci gaba da yin shiru ta fuskar diflomasiyya kan irin waɗannan abubuwa na iya ƙarfafa masu aikata su.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kwashe sama da ‘yan Najeriya 1,490 daga Afirka ta Kudu ta hanyar jigilar jirage bakwai domin kare rayukansu sakamakon rikice-rikicen.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na tattaunawa da Ghana domin haɗa kai wajen matsa wa Tarayyar Afirka lamba ta ɗauki matakin hukunta Afirka ta Kudu kan ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi.

An bayyana cewa hare-haren ba ‘yan Najeriya kaɗai suka shafa ba, har ma da dubban ‘yan wasu ƙasashen Afirka da ke zaune da aiki a Afirka ta Kudu.

A wani ɓangaren kuma, Shugaba Tinubu ya sake jaddada aniyar Najeriya na goyon bayan shirin ECOWAS Compact for the Future of Regional Integration, wanda ke da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasashen yankin, inganta shugabanci nagari, bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashe, da samar da kasuwar hada-hadar yanar gizo guda ɗaya domin faɗaɗa damar ayyukan yi ga matasa.

Ya ce tabbatar da shugabanci nagari da kare rayuka da haƙƙin ‘yan Afirka su ne manyan ginshiƙan samar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shari’ar Ta’addanci: Manyan Jagororin Ansaru Biyu Sun Amsa Laifi A Abuja
Next Post: Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Fabrairu Labarai
Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Djibouti Yau Juma’a Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • Yau Lahadi Ake Gudanar Da Zabe A Kasar Myanmar Labarai
  • Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
  • Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.