Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin
Published: December 7, 2025 at 10:13 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 8, 2025

Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan kare demokuraɗiyya a Jamhuriyar Binin.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkinsu na dimokuraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar da safiyar Lahadi.

A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Binin ta aikawa Najeriya da buƙatu biyu na gaggawa, ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, tana neman a turo da jiragen yaƙin saman Najeriya domin kwace tasoshin da sojojin da suka yi juyin mulkin suka mamaye, ciki har da Talabijin na ƙasa da kuma wani sansanin soja.

Najeriya ta amsa wannan kira nan take, inda Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta NAF ta shiga sararin samaniyar Binin domin kawar da barazanar.

Haka kuma gwamnatin Binin ta roƙi a tura ƙarin jiragen leƙen asiri da kuma sojojin ƙasa na Najeriya, domin taimaka musu a ayyukan tsaro da kariyar manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin hukumomin tsaron Binin.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan bukatun da ƙasar Binin ta nema, ciki har da zuwan sojojin Najeriya cikin ƙasar.

Yunƙurin juyin mulkin dai ya faru ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanar Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da muhimman hukumomin dimokuraɗiyya.

Sai dai da taimakon dakarun Najeriya, jami’an gwamnati masu biyayya ga Shugaba Talon sun kwace tashar Talabijin ɗin da sauran wuraren da aka mamaye, lamarin da ya kawo ƙarshen yunkurin juyin mulkin.

Da yake martani bayan tabbatar da dawowar tsarin dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya bisa rawar da suka taka.

“A yau, rundunar sojin Najeriya ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin mulki a Jamhuriyar Binin bisa gayyatar gwamnatin ƙasar. Sun yi aiki bisa ka’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Binin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciya hankali a yankin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba”
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Ceto Wasu Daliban St. Mary’s

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026 Shirye-Shirye
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
  • Kasashe 5 Da Ke Fama Da Matsanancin Zazzabin Cizon Sauro Rediyo
  • Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
  • Ceto ɗaliban Neja An Samu Natsuwa A ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai Labarai
  • Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.