A kalla mutane 38 a jihohin Amurka 14 ne suka rasa rayukansu zuwa ranar Talata sakamakon yanayin sanyi mai tsanani da ya lullube yawancin tsakiya da gabashin kasar da dusar kankara, tare da daskararriyar kankara, a cewar jami’ai da kuma rahotanni daga kafofin yada labarai.
Yanayin tsananin sanyin ya fara ne ranar Juma’a, inda ya jibge dusar kankara a fadin sashe me girma na kasar, a karshen mako. Dusar kankarar ta jawo tsaikon zirga zirgar ababen hawan titi, kuma ta jawo An soke tashin jiragen sama. Ta kuma haifar da daukewar wutar lantarki, kafin ta lafa ranar Litinin, inda ta bar sanyi da ake ganin zai dade.
Zuwa ranar Talata, birane sun fara harhado kan masu bada agaji, domin tabbatar da cewa mazauna, musamman ma marasa matsuguni basa cikin matsala, a yayin da fiye da gidaje 550,000 da wuraren kasuwanci ke fama da rashin wutar lantarki a fadin kasar.
Cikin mutanen da suka rasa rayukan su, goma sun fito daga birnin New York, inda sanyi yayi tsananin da bai taba yi ba cikin shekaru 8, a cewar magajin gari Zohran Mamdani a wani taro na manema labarai ranar Talata, lokacin da yanayin sanyi ya kai digiri 8 a ma’aunin fahrenheit.
Duk da cewa mamatan 10 an same su ne a waje, ba’a samu damar tantancewa ko basu da matsuguni ne ba. Mamdani ya shaidawa Manema labarai ranar Litinin cewa wasu daga cikin mamatan sun yi alaka da wuraren bada mafaka a da, amma yayi wuri ace za’a fayyace abinda ya haddasa mutuwar tasu.


