Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye
Published: April 13, 2026 at 6:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon jagoran masu kishin ƙasa na Hungary, Viktor Orban, ya amince da shan kaye a jiya Lahadi bayan babbar nasarar zaɓe da sabuwar jam’iyyar adawa ta Tisza ta samu, lamarin da ya zama koma baya ga abokan hulɗarsa a Rasha da kuma Fadar White House ta Shugaban Amurka Donald Trump.

Sakamakon zaɓen da aka samu bisa ƙididdigar kashi 81.5% na ƙuri’un da aka kirga ya nuna cewa jam’iyyar Tisza mai ra’ayin tsakiya ta dama kuma mai goyon bayan Tarayyar Turai (EU), ƙarƙashin jagorancin Peter Magyar, ta lashe kujeru 137, wanda ya ba ta rinjaye mai muhimmanci na kashi biyu bisa uku a majalisar dokoki mai mambobi 199, inda ta kayar da jam’iyyar Fidesz ta Orban.

“Sakamakon zaɓen bai kammala ba tukuna, amma halin da ake ciki a bayyane yake kuma a fahimce yake,” in ji Orban mai shekaru 62 a ofishin yakin neman zaɓe na Fidesz. Wasu daga cikin magoya bayansa da suka taru a wajen ofishin sun fashe da kuka yayin da suke kallonsa yana jawabi a talabijin.

Inda yace “Sakamakon zaɓen yana da raɗaɗi a gare mu, amma a bayyane yake.”

Labarai, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Yiwuwar Iran Da Amurka Su Cimma Matsayar Dakatar Da Shirin Nukiliya Amurka
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Shugaban Ƙasar Djibouti Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Afrika
Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Baitul Malin Amurka Zata Bawa Venezuela Da Cuba Damar Sayar Da Mai Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye
  • Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi
  • Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya
  • Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran
  • Amurka Da Iran Sun Tattauna A Kasar Pakistan

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • Man Da Matatar Dangote Take Fitarwa Zuwa Kasashen Afirka Ya Karu Afrika
  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
  • Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
  • Farashin Danyen Mai A Amurka Ya Tashi Afrika
  • Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
  • Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.