Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce ya tattauna na tsawon awa daya dazun nan da wakilin shugaba Donald Trump na Amurka, Steve Witkoff, da kuma surukin shugaban Jared Kushner, a kan yadda za a kawo karshen yakin Ukraine.
Shugaba Zelensky ya wallafa a shafinsa na Telegram cewa tattaunawar tasu ta yi kyau, inda suka yi musayar ra’ayi kan dalla-dallar matakan da za a dauka.
Ya ce an gabatar da sabbin ra’ayoyi a kan yadda za hanzarta kawo zaman lafiya na gaskiya, abinda yace ya kunshi tsarin da za a bi, da tattaunawar da za a yi, sai kuma abu mai muhimmanci wanda shine lokacin da za a aiwatar da su.


