Gidauniyar Alhaji Dahiru Barau Mangal, wato Mangal Foundation, ta fara gudanar da tiyatar cutar Hernia da Hydrocele kyauta ga mutane sama da 800 a jihar Katsina.
An fara aikin ne a Babban Asibitin Katsina ranar Juma’a 12 ga Disamba, 2025, bayan kammala tantance mutanen da ke fama da cututtukan a kwanakin baya.
A yayin tantancewar, an gano mutane da dama da ke bukatar tiyata, inda gidauniyar ta dauki nauyin aikin kyauta, ba tare da wadanda suka amfana sun biya ko sisi ba.
Da yake jawabi yayin fara aikin, ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Hussaini Kabir, ya bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da tiyatar har zuwa ranar Lahadi.

Alhaji Hussaini Kabir ya kara da cewa, bayan an yi wa marasa lafiya aikin, gidauniyar za ta ci gaba da daukar nauyin kulawa da su da magunguna har zuwa lokacin da za a sallame su daga asibiti.
Ya bayyana cewa, a lokacin tantancewar, an duba daruruwan mutane masu fama da matsalolin lafiya daban-daban, inda da yawa daga cikinsu aka ba su magunguna kyauta aka kuma sallame su.
Alhaji Kabir ya jaddada cewa wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar ke gudanar da irin wannan aiki ba, yana mai cewa a duk shekara ana shirya irin wannan aiki domin tallafawa al’umma.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin sun bayyana godiya da addu’o’i ga shugaban gidauniyar, bisa wannan tallafi.
Sun kuma yi kira ga gwamnatoci, kamfanoni da masu hannu da shuni da su yi koyi da gidauniyar wajen tallafa wa marasa galihu a fadin kasar.


