‘Yan ta’adda sun hallaka a kalla sojoji 12 da farar hula uku a wani hari da suka kai cikin dare a arewa maso gabashin Nigeria, a cewar majiyoyi daga sojoji da kuma mazauna wurin ranar Litinin.
Harin ya auku a garuruwan Kukawa da Dalwa a jihar Borno, da kuma Goniri a jihar Yobe kuma ya biyo bayan wani harin da aka kai kwanaki garin Ngoshe.
Kungiyar Boko Haram sun farwa Kukawa kafin wayewar garin ranar Litinin, suka durfafi sansanin soji dake wajen, inda aka shafe sa’o’i uku ana musayar wuta. Daga bya sojoji sun yi nasara, amma kwamandan rundunar da wasu sojoji biyar sun rasa rayukan su. Dan majalisa mai wakiltar Kukawa, Karta Ma’aji, ya tabbatar da aukuwar harin.
A Dalwa kuma ‘yan ta’addan sun kashe sojoji biyu da farar hula uku, sannan suka kona gidaje 250. A Goniri kuma da ke jihar Yobe, nan ma sun kai hari sansanin soji, inda suka hallaka sojoji hudu, suka kuma kone motocin wurin.


