Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu
Published: January 28, 2026 at 11:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan uwan wasu mutane 2 da aka kashe sakamakon harin da sojin Amurka suka kai wani jirgin ruwa da ake zaton na dauke da muggan kwayoyi, da ya taso daga Venezuela sun kai kara gaban kotu kan yiwa ‘yan uwan nasu kisan sakaci ranar Talata. Sun yi ikirarin cewa an kashe ‘yan uwan nasu ne ta hanyar da ta sabawa doka, ta yadda sojoji ke harin jiragen ruwan farar hula.

Lawyoyin masu rajin kare hakki, sun gabatar da karar ne a wata babban kotun kasa ta Amurka da ke birnin Boston. Karar da ta kasance ta farko da aka gabatar tun tun da Amurka ta kai hari har sau 36 kan jiragen ruwa a tekun Carribean da na Pacific, bisa umarnin gwamnatin Donald Trump, abinda yayi sanadiyyar rayuka 126 tun watan Satumbar bara.

‘Yan uwan Chad Joseph da Rishi Samaroo, mutane biyu ‘yan kasar Trinidad, na daga cikin mutane 6 da aka kashe a wani hari da aka kai ranar 14 ga Watan Oktoba. karar da aka gabatar ta ce mutanen biyu suna noma ne da kamun kifi a Venezuela, kuma suna hanyar su ta komawa gida ne a Las Cuevas da ke Trinidad yayin da aka kai musu harin.

Lauyan masu gabatar da kara Brett Max na ofishin masu rajin kare hakki na American Civil Liberties Union, ya ce wannan kisa ne da bashi da hujja daga gwamnatin dake cin zarafin ikon mulki ba tare da fuskantar hukunci ba, kuma wannan kara da aka gabatar na bukatar bin hakki da kuma kare dokokin shari’a.

Kungiyar lauyoyin rajin kare hakki sun gabatar da karar ne karkashin dokar Mutuwa a Teku mai Zurfi (wato Death on High Seas Act) a turance, dokar da ta bawa ‘yan uwan mamata damar kai kara don kisan sakaci ga ‘yan uwan su da ya auku a babban teku ko teku me zurfi, da kuma dokar kisa ga baki (Alien Tort Statute), ta shekarar 1789, wadda ta bawa bakin haure damar kai kara gaban kotunan Amurka, idan Amurkan ta saba dokar kasa da kasa.

Mahaifiyar Chad Joseph, Lenore Burnley, da kuma ‘yar uwar Rishi Samaroo, Sallycar Korasingh ne suka kai karar, kuma suna neman diyya ne kawai daga gwamnatin Amurka kan kisan ‘yan uwan nasu, ba wai kotu ta bada umurnin hana kara kai hare-haren nan gaba ba.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Tsananin Sanyi Ya Kashe Mutane 38 A Amurka
Next Post: Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
Akwai Alamar Shawarwari Tsakanin Amurka Da Turai Zai Kawo Karshen Yakin Rasha Amurka
Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana Afrika
Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka
Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Tinubu: Munsayi Jiragen Yaki Daga Wajen Amurka Amurka
  • Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum Tsaro
  • Gwamnatin Gombe: Babu Hannun mu a Cin Zarafin Kansilan Mazabar Shamaki Siyasa
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Yau Litinin Ake Cigaba Da Shari’ar Najib Zarak Labarai
  • An Farmaki ‘Yan Bindiga Da Dama A Jihar Zamfara Labarai
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
  • Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.