Gwamnatin Amurka ta yi wani garon bawul ta samun visa ga ‘yan Najeriya a wasu rukuni na visa kasara, a cewar Fadar Shugaban Amurkan,
Gwamnatin Donald Trump ta kakabawa ‘yan Najeriya masu niyyar kawo ziyara Amurka takunkumi na hana su shiga kasar, inda ta ce bata samun issassun, kuma gamsassun bayanai daga masu bincike kan matafiyan.
Sabon takunkumin ya hana ‘yan Najeriya da ke neman takardar zama na dundundun, ko masu neman visa na zuwa kasuwanci B-1, ko kuma yawon bude ido, B-2, da kasuwanci da yawon bude ido B-1/B-2, da ta karatu a makarantu F, ko kuma zuwa karo ilimin da bai shafi makarantu ba M, da kuma na masu zuwa na shirin musayar ra’ayi J.
Wannan ya na nufin an haramtawa ‘yan Najeriya da ke dauke da wadannan visar ta B-1. A yayin da gwamnatin Donald Trump ta ke ci gaba da nuna tsatsauran ra’ayi kan yin kaura zuwa kasar, kuma ta saka tsauraran matakai kan visa zuwa aiki ta H-1B, wani dan kasuwa haifaffen kasar India, ya shiga jerin masu kudi a sashen fasahar kwamfuta a Amurka. An Haifi Jyoti Bansal, wanda ya samar da kamfanin Fasahar AI mai suna Harness, a Rajasthan, kuma ya yi karatun sa ne a ITT Delhi.
Jyoti Bansal, wanda ya yi kaura zuwa Amurka daga India, da kudi kadan a aljihun sa dauke da visar damar yin aiki a Amurka, ya zama sabon bilonoya bayan da kamfanin sa na Harness ya tara dala miliyan 240,000, da hannun jarin sa kuma ya kama kan dala biliyan biyar da rabi (5.5), a cewar wani rahoto da mujallar Forbes ta wallafa.
Bansal ya kasance mai suka ne ka dokokin shige da fice na Donald Trump, inda ya ce suna dakile samun masu kwazon da suka dace ga Amurka.
Daga karamin garin a Rajasthan zuwa gagarumar nasara a fadar fasahar kwamfuta ta duniya, wannan daukaka ta Bansal na daga cikin misalai na baki dake zuwa basu da komai suna samun daukaka a Amurka, kawai don saboda naci da jajircewa.
Jyoti Bansal ya girma ne a wani karamin gari a Rajasthan, indayake taimakawa babansa wajen kasuwanci injinan yin noma.
Kwazon sa a makaranta ya bashi damar zuwa jami’ar ITT Delhi, inda ya karatun injiniya a fannin kwamfuta. Yana shekara 21 ya yi kaura zuwa Amurka da guzuri kada, amma da babban buri. Ya shafe kusan shekara 10 yana aiki a matsayin injiniya a kamfanoni uku da suka sama masa visar H1B, ta nan ya samu ra’ayin muhimmanci barin mutane masu fasaha shigowa Amurka don ta ci gaba da zama zakaran gwajin dafi a duniya.


