Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa
Published: December 9, 2025 at 7:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Gwamnonin jihohin arewa ta Naɗa Ezekiel Gomos a matsayin babban darakta don karfafa haɗin kan yankin

Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ta amince da naɗin Mista Ezekiel Gomos, OFR, a matsayin Babban daraktan sakatariyar ƙungiyar.

Naɗin dai ya yi daidai da sabbin alƙawuran da ƙungiyar ta ɗauka na ƙarfafa ayyukan hukumominta da inganta haɗin kai a tsakanin jihohin Arewa 19 wajen tinkarar ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

A cewar ƙungiyar, samar da ofishin Babban Daraktan wani kyakkyawan mataki ne na mayar da Sakatariyar ya zuwa cibiya mai inganci wajen haɗa kai da inganta manufofi, da aiki tare da kuma samar da tsare-tsaren ci gaba na dogon zango.

Mista Gomos, wadda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Filato ne, ƙwararre ne a fannin tattalin arziƙi, siyasa da aikin gwamnati, da kuma inganta harkokin mulki, da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu da kuma ciyar da jama’a gaba.

Ƙwarewarsa ta haɗa da manyan ayyuka a manyan cibiyoyi masu tasiri irin su New Nigeria Development Company (NNDC) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afirka (WAEC).

Bugu da ƙari, ya kasance ƙwararren mai bada shawara kuma shugaban tsangaya a Makarantar Kasuwanci ta Jos (JBS), makarantar data mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin kasuwanci, horas da shugabanni da tsare-tsaren manufofi.

Mista Gomos ya shafe kusan shekaru ashirin yana aiki a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa (NIPSS) dake Kuru, inda ya bada gudummawa wajen horar da manyan shugabanni a faɗin Najeriya ta fuskar manufofi, dabaru da ci gaban ƙasa.

Sauran harkokin karatu na sabon Babban Daraktan sun haɗa da digiri na ɗaya dana biyu da ya yi a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya da kuma Jami’ar East Anglia ta kasar Birtaniya.

Har ila yau mamba ne a wasu manyan cibiyoyi na duniya, ciki har da Hubert Humphrey Fellowship (na Jami’ar Minnesota) da Chevening Scholarship na Birtaniya da kuma kasancewarsa mamba a hukumar ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP Fellowship) a Cibiyar Horaswa ta Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) a Turin.

Gomos ya halarci manyan horaswar shugabanci a Makarantun Harvard Kennedy, da Jami’ar Chicago Booth School of Business, da Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Durham.

Da yake gabatar da takardar naɗin, Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Mista Gomos ya yi amfani da ƙwarewarsa ta fannin jagoranci dabaru, ci gaban cibiyoyi da tsare-tsare don ƙarfafa sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin ta Arewa zuwa wata katafariyar dandalin haɗin gwiwar tsaro da tattalin arziƙin yankin da kuma ci gaba mai ɗorewa a faɗin Arewa.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa naɗin zai haifar da wani sabon yanayi na zurfafa haɗin gwiwa, da ingantaccen haɗin kai da kuma samar da matakan da suka dace da yankin don fuskantar ƙalubalen Arewa.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu
Next Post: Gwamna Fubara: Rashin Kariya daga PDP Ne Ya Tilasta Ni Komawa APC

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya
Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika
Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Farmaki ‘Yan Bindiga Da Dama A Jihar Zamfara Labarai
  • Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Abubakar Malami Bisa Wasu Sharruda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika
  • CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
  • Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
  • Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.