Shugabanin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun fara gudanar da taron kolin kungiyar AES a wannan litinin 22 ga watan disamban 2025 da nufin tattauna batutuwa da dama da suka shafi yankin da rayuwar al’umomin kasashen 3 masu fama da matsaloli iri daya musamman aika aikar kungiyoyin ta’addanci. wasu ‘yan Nijar suka fara bayyana fatansu kan wannan taro kamar yadda za a ji a wannan rahoto da wakilin GTA Hausa Amurka ke Magana Souley Moumouni Barma ya aiko mana daga Yamai.
Janar Abdourahamane Tiani na Nijar da Keftin Ibrahim Traore na Burkina Faso da Assimi Goita na Mali shugaban rikon kungiyar AES a yayin zaman na wuni biyu za su yi bitar ayyukan hadin guiwar da suka gudanar a kungiyance kafin su tattauna kan batutuwan da zasu fi baiwa fifiko a nan gaba musamman ta inda za su bullowa lamarin tsaro, tattalin arziki aiyukan ci gaban jama’a diflomasiya da dai sauransu. shin ko ya ‘yan Nijar ke kallon wannan taro.?
Koda yake yanayin tsaro na kan gaban abubuwan da aka fi nuna damuwa kansu, ‘yan fafutika irinsu Hamidou Sidi Fody na kungiyar kulawa da Rayuwa na shawartar shugabanin kasashen 3 su kuma kara duba wata matsalar ta daban da ke dabaibaye harakokin tattalin arziki.
Nijar da Mali da Burkina Faso na cikin wata fafutikar tabbatar da ‘yancin kai a yayin da alamu ke nuna bayyanar babban sauyi a tafiyar siyasar duniya ta yau. abin da ke kara wa jama’ar yankin AES kwarin guiwa a game da manufofin da shugabanin kasashen 3 suka sa gaba sai dai akwai abin lura.
kungiyar AES ta samo asali a watan satumban 2023 kafin ta zama gamayya bayan watanni biyu da zumma duba alkibla guda a game da dukkan batutuwan da suka shafi tsaro diflomasiya tattalin arziki da sauransu, kasashen 3 sun fice daga CEDEAO a janerun 2024 saboda zargin kungiyar da zama ‘yar amshin shatan kasashen yammaci. sannan sun kori sojojin Faransa daga yankin sahel. daga bisani sun kafa rundunar hadin guiwa mai dakaru 5000 wace a karshen makon jiya aka kaddamar da aiyukanta a hukumance a ci gaba da jan damarar yaki da kungiyoyin ta’addanci.


