Bam ya tashi cikin wani masallaci a lokacin sallar magariba jiya da daddare a wata kasuwa dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya kashe mutane akalla 5, ya raunata wasu fiye da 30.
‘Yan sanda sun ce watakila harin na kunar-bakin-wake ne, inda kakakin ‘yan sandan jihar, Nahum Daso ya fada cikin wata sanarwa cewa an samu abinda ya rage na wata rigar da ake zaton ta kunar bakin wake ce.
Wannan harin shine na baya bayan nan a yankin arewacin Najeriya, inda ake fama da ‘yan ta’addar Boko Haram da na ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar, da kuma kungiyoyin barayi da ‘yan fashin daji dake satar mutane suna garkuwa da su a yankin arewa maso yamma.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin ya zuwa yanzu, amma an fi alakanta harin kunar bakin wake da kungiyar Boko Haram.


