Farashin man fetur ya fadi ranar Laraba, kuma an samu asarar kusan kashi 20 cikin 100, a yayin da sa rai da ake yi na samun man da yawa ya karu, a shekarar da ta ga yake-yake, karin kudin kayayyakin shiga, karin mai daga kasashe masu arzikin mai na OPEC da sauran su, da kuma takunkumi da aka sawa kasashen Rasha, Iran da Venezuela.
Kamfanin Brent Crude Futures ya ragu da kimanin kashi 19 cikin 100 a shakarar 2025, kuma ta kasance shekara ta 3 kenan a jere, yana asara, wanda shine lokaci mafi tsawo da aka taba samun irin haka, shima kamfanin Amurka na West Texas Intermediate Crude ya ragu da kashi 20 cikin dari a shekara.
A ranar karshe na shekarar 2025 da ta wuce, Brent Crude Futures yana sai da ganga daya ta mai kan farashin dala 60 da kobo 85, inda farashin ya yi kasa da kobo 48, yayin da farashin gangar mai a West Texas Intermediate Crude kuma ya fadi da kobo 53, inda ko wacce ganga ta tashi kan dala 57 da kobo 42.


