Mexico ta bada labarin samun karin wata dabba da take fama da cutar tsutsa, wannan shine na biyu a cikin kwanaki biyu da hukumomin kasar suke bada rahoto kan haka, yayinda kasar take kokarin shawo kan wannan matsala data sa aka hana dabbobi daga Mexico tsallakawa Amurka.
Wata hukumar kasar mai kula da lafiyar dabbobi tace an gano tsutsar ce a jikin wata akuya, aka bata magani, an auna wasu awaki ashirin dake a wannan garke, aka samu basu harbu ba, kuma aka basu maganin riga kafi a jihar Mexico, mai makwabta da babban birnin kasar.
Kamar yadda alkaluma daga gwamnatin kasar suka nuna, Mexico ta bada rahoton wannan matsala har dubu 13,106 daga nuwamban shekara ta 2024, zuwa 31 ga watan disamba shekara ta 2025 a cikin wannan adadi 671 har yanzu ana jinyar su.


