Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa siyasar sa za ta shiga mummunan hali matuƙa idan Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya samu wa’adi na biyu a mulki.
Wike ya faɗi hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a wani taro da aka gudanar a ƙaramar hukumar Okrika dake jihar Rivers.
Ko da yake ministan bai ambaci sunan gwamnan kai tsaye ba, ya jaddada cewa an riga an yanke shawara mai ƙarfi dangane da zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Wike ya ce: “Mun riga mun yanke shawara dangane da Tinubu, Amma wancan (sake zaɓen Fubara) babu yadda za a yi, Domin idan muka sake yin kuskure, to mun je mun binne kanmu a siyasa kuma, Ba zan bari a binne ni ba, Ba zan sake yarda a yi irin wannan kuskuren ba.
“Don haka kowa ya sani mun riga mun yanke shawara.”
Ministan Abujan ya ƙara tsananta sukar sa ga Fubara tun bayan da gwamnan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a watan da ya gabata sannan wike ya zargi gwamnan da saba sharuɗɗan yarjejeniyar sulhu da aka cimma kafin a ɗage dokar ta baci a jihar, wadda ta ba da damar Fubara ya koma kan kujerar sa.


