Hukumomin Uganda sun yanke hanyar sadarwa ta internet, kuma suka dakile hanyoyin wayar tarho a fadin kasar ranar Talata, kwanaki biyu kafin zaben da shugaba yoweri Museveni ke neman zarcewa a karo na 7, bayan da ya shafe shekaru 40 yana mulki.
Ma’aikatar sadarwa ta Uganda ta bawa kamfanonin da ke samar da internet umarni da su rufe hanyar sadarwa daga karfe 6 ranar Talata domin magance yada jita-jita, da labarun karya, madugun zabe, da sauran abubuwan da zasu haifar da nakasu wajen gudanar da zaben, kunshe a wata wasika da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya samu dubawa.
Jami’an tsaro sun kame daruruwan magoya bayan jam’iyyun adawa, kafin zaben kuma sun harba bindigogi da tear gas lokacin taron gangamin nuna goyon baya ga babban me kalubalantar Museveni, Bobi Wine.


