An kaddamar da shirin rajistar mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hanyar zamani a jihar Gombe, karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya.
Da yake kaddamar da shirin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci daukacin mambobin jam’iyyar da su koma mazabunsu domin yin rajistar yadda ya kamata ya kuma jaddada cewa mallakar Katin Zabe na Dindindin (PVC) da Katin Shaidar Dan Kasa (NIN) su ne muhimman sharuɗɗan samun cikakken rajista a jam’iyyar.

Gwamnan ya kuma yaba da irin namijin kokarin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen ci gaban kasa da kuma karfafa matsayi da farin jinin jam’iyyar APC.
A nasa bangaren, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Gombe, Nitte Amangal, ya tabbatar da cewa aikin rajistar zai gudana a dukkan mazabu 114 da ke fadin jihar, tare da bukatar mambobi su yi rajista a inda suka fito.


