Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Mayakan RSF Sun Zafafa Kai Hare Hare Da Jirgi Maras Matuki A Sudan
Published: January 23, 2026 at 2:02 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A Sudan mayakan RSF ko Rapid Support Forces da turanci sun zafafa kai hare hare da jiragen yakin da babu matuka da ake kira Drones da turance a ciki da kewayen birnin al-obeid da ke tsakiyar Sudan, a yayinda yakin basasar yake kara kusa da birnin da yake karkashin sojoji, wadda ya haddasa hasarar rayuka farar hula masu yawa, a lokuta daban daban har sau biyu, kamar yadda mazauna birnin suka fada.

Birnin yana da muhimmancin gaske, kuma shine babban birnin jihar Kordofan, birni da ya raba yankin na Kordofan da yankin Darfur dake hanun ‘yan tawaye, da kuma gabashin kasar dake hanun sojojin Sudan.

Rahotanni suka ce bayan da ‘yan tawayen na RSF suka kama yammacin yankin Darfur cikin watan Oktoba, yanzu sun maida hankalin su yankin kordofan, kuma a duk mako sai sun kai hari a da jiragen Drones, kamar yadda mazauna yankin suka fada.

Zuwa yanzu dakarun na RSF basu tunkari al-obeid kai tsaye ba, inda jama’a suke ci gaba da harkokin su na yau da kullum duk da barazanar suke hangowa.

Sojojin Sudan da masu mara musu baya, sun kama wuri bayan birnin na a-Obeid.

A halinda ake ciki kuma, wata kungiyar tallafawa yara da ake kira Save the Children da turanci, tace fiye da yara miliyan 8 ne da suka kai shekarun Shiga makaranta da a halin yanzu basa karatu, sakamakon yakin basasar da kasar take famada shi.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista
Next Post: Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine

Karin Labarai Masu Alaka

CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci Afrika
An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Real Madrid Ta Sauya Tsarin Gabatar Da Mourinho Da Sabbin ’Yan Wasanta A Santiago Bernabéu Wasanni
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
  • Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
  • Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
  • Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.