Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba
Published: November 21, 2025 at 5:05 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Shugaba Umaro Sissoco Embalo na kasar Guinea-Bissau, yana fuskantar kalubale sosai a zaben shugaban kasar da ake shirin yi a kasar jibi Lahadi, yayin da aka ce kasar tana kara zamowa zangon masu safarar hodar iblis ta Cocaine daga kasashen kudancin amurka.

Babban mai adawa da shi, shine Fernando Dias na jam’iyyar PRS, wanda mutane masu yawa suka fara halartar kyamfe nasa a yayin da yake alkawarin karfafa tsaro da sasantawa da kuma hana sojoji yin katsalanda a harkokin siyasa a wannan kasa da ta saba ganin juye juyen mulkin soja.

Duk da cewa akwai ‘yan takara 12 a wannan zabe na jibi, shugaba Embalo mai shekaru 53 da haihuwa da kuma Dias, sune ake kyautata zaton dayansu zai lashe zaben.

Ana sa ran jin sakamakon farko cikin kwanaki biyu da zaben. Idan babu dan takarar da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri’u, to za a je ga zagaye na biyu tsakanin ‘yan takara biyu da suka fi samun kuri’u.

A halin da ake ciki, kasar ta Guinea-Bissau, tana kara karfafa matsayinta na muhimmin zangon safarar hodar iblis ta Cocaine da ake daukowa daga kudancin Amurka zuwa kasashen Turai.

Wani masani a faransa yace ana kara samun shaida cewar Guinea-Bissau tana jaddada matsayinta na zangon safarar muggan kwayoyi a yayin da ake kama ‘yan kasar dauke da hodar Iblis ta Cocaine a yankin da kuma a kasashen ketare.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Nnamdi Kanu Zai Daukaka Kara Har Zuwa Kotun Koli
Next Post: ‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary!

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Tace Jakadan Kasar Ta A Lebanon Zai Cigaba Da Zama A Beirut Afrika
Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
RSF Ta Nemi A Gaggauta Gano Dan Jarida Moussa Kaka Da Ya Bace A Yamai Afrika
Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli Afrika
  • Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Amurka Na Zargi Kasar Rwanda Da Kokarin Saba Yarjejeniyar Zaman Lafiya Amurka
  • Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
  • Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika
  • Sudan Takai Hari Kasar Chadi Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • Magoya Bayan Tijjaniyya Zasu Kauracewa Zabe Saboda Kama Sheikh Sani Khalifa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.