Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata
Published: February 14, 2026 at 3:58 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa dangane da bacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

A wata sanarwa da tsohon Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamared Muhammad Garba, ya sanya wa hannu, Ganduje ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, tare da cewa yunƙuri ne na karkatar da alhakin abin da ya faru a jihar Kaduna kaɗai.

Sanarwar ta jaddada cewa Dadiyata ya rayu kuma ya gudanar da harkokinsa ne a Kaduna, inda aka san shi da sukar gwamnatin jihar a wancan lokaci.

A cewar sanarwar, babu wata hujja da ke nuna cewa ya fi mayar da hankali kan gwamnatin Kano ko kuma kan Ganduje.

Tsohon gwamnan ya buƙaci a yi nazari mai zurfi kan kalaman El-Rufai, yana mai cewa irin waɗannan manyan zarge-zarge ya kamata su kasance tare da hujjoji masu inganci, ba wai furucin siyasa kawai ba.

Ganduje ya kuma bayyana cewa jawo sunansa cikin lamarin ba tare da tabbatacciyar shaida ba na iya rikita jama’a kan batun da har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin mulkinsa na wa’adi biyu a Kano, an san gwamnatin Ganduje da karɓar suka, hulɗa da kafafen yaɗa labarai, da kuma bai wa ’yan adawa damar bayyana ra’ayoyinsu ba tare da tsangwama ba.

Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa
Next Post: INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
Gwamna Abba Kabir Ya Zabi Garo A Matsayin Mataimaki Afrika
Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
Kasar Rasha Ta Zargi Ukraine Da Kai Hari Gidan Shugaban Rasha Amurka
Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai Sauran Duniya
  • Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump Amurka
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
  • EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
  • Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar Afrika
  • Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
  • NFF Ta Nemi Afuwar Tinubu Da ’Yan Najeriya Kan Rashin Samun Tikitin Zuwa Gasar Kofin Duniya Ta Mata Wasanni
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.