Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato
Published: March 16, 2026 at 8:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Al’ummar kauyen Wanka dake karamar hukumar Kanam a Jihar Filato sun nemi hukumomi su kai musu dauki, bayan watsewarsu daga kauyen, biyo bayan kisan sojoji da ‘yan banga da ‘yan ta’adda suka yi a karshen makon jiya.

Garin Wanka, wanda ke yankin Garga a karamar hukumar Kanam a jihar Filato, na makwabtaka da karamar hukumar Alkalerin jihar Bauchi kusa da dajin da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Wani mazaunin garin na Wanka da ya bukaci in sakaya sunanshi saboda tsaro, yace ‘yan bindigar sun kashe sojoji goma sha hudu da ‘yan banga biyar, lamari kenan da ya sanya suka watse daga kauyen.

Duk da cewa kafafen yada labarai sun yayata batun kisan sojojin, rundunar dake wanzadda zaman lafiya a yankin, Operation Enduring Peace bata fitar da sanarwa kan batun ba.

Bayanai sun nuna cewa sojojin da aka kashen suna aikin tabbatar da tsaro ne a yankin, kafin ‘yan bindigar su yi musu kwanton bauna suka hallaka su.

Haka ma bayanan da ba’a tantance ba sun nuna cewa sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda fiye da ishirin a yankin na Wanka.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar Filato ta fitar da sanya hannun komishinan yada labarai da sadarwa, Madam Joyce Ramnap tace gwamnati na kan bakanta na tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

Sanarwar tace gwamnati ta hada gwiwa da jami’an tsaro don kara azama wajen tabbatar da tsaro a dukkan yankunan dake fuskantar barazanar tsaro a fadin jihar.

Mai fashin baķi kan lamura kuma sakataren kungiyar dake raya al’ummar Kanam, Nuhu Shehu Kanam yace matsalar tsaro a yankin ba sabon abu bane amma hukumomi sun kasa shawo kanta.

Bayanai na nuni da cewa ayyukan masu bada bayanai wa ‘yan ta’adda, da aka fi sani da informants, suna tasiri wajen samun cikkas da yaki da matsalolin tsaro a yankin na Garga da kewaye.

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AUD-20260316-WA0040.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu
Next Post: Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 A Kasar Australiya Labarai
Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano! Najeriya
An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe Najeriya
Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
  • Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
  • Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya Afrika
  • AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
  • Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.