Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026
Published: November 26, 2025 at 3:23 PM | By: Nafisa Ahmad

Da alamun Cristioano Ronaldo zai buga ma Portugal dukkan wasanninta a gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta shekara mai zuwa, duk da jan katin da aka ba shi lokacin da ya buge wani dan wasan Ireland da gwiwar hannu.

A yau Talata hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta wallafa hukumcin dakatar da shi daga wasanni uku da ta yanke, amma ta ce wasa daya dole zai rasa, sauran biyu kuma an dage hukumci a kansu har na tsawon shekara guda domin a ga ko zai sake aikata irin abinda yayi har aka ba shi jan katin.

An dakatar da Ronaldo daga buga wasa guda na tilas a lokacin da kasarsa ta buga da Armeniya ta lashe da ci 9-1, abinda ya tabbatar da gurbinta a gasar cin kofin duniyar da za a yi a nan yankin nahiyar Amurka ta arewa a shekara mai zuwa.

Masu fashin baki da dama sun dauka cewa za a dakatar da Ronaldo daga karin wasa guda, ta yadda za a fara buga gasar cin kofin duniyar ba tare da shi ba.

Wannan shine karo na 6 da Ronaldo zai buga ma Portugal kwallo a gasar cin kofin duniya, abinda babu wani dan wasan da ya taba haka.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL
Next Post: Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025. Wasanni
An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci Wasanni
Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba” Wasanni
Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
  • Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
  • Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • Dakarun Gwamnatin Kasar Sham Tayi Mamaya Zuwa Gabashin Kasar Labarai
  • Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.