Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Kasar Ghana
Published: March 27, 2026 at 7:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin da kasar Ghana ta gabatar a ranar Laraba na ta yarda da bautar da mutane a ketaren tekun Atlantika a matsayin laifi mafi muni ga dan Adam, kuma an yarda da kudurin neman diyya, duk da bijirewa da aka samu daga Turai da kuma Amurka.

Ghana tace ana bukatar wannan kuduri, saboda abunda bautar da mutane ya haddasa, inda aka dauki a kalla mutanen Afrika miliyan 12 da dubu 500, aka sayar da su tsakanin karni na 15 zuwa karni na 19, har yau ana fuskantar sa, ciki har da wariyar launin fata.

A kuri’ar da aka kada a babban taro na Majalisar Dinkin Duniya, kasashe 123 sun goyi bayan kudurin, uku kuma basu goyi baya ba, cikin su akwai Amurka da Isra’ila, sannan kasashe 52 basu kada kuri’a ba, ciki da Tarayya Turai da Birtaniya.

Justin Howard, Ferfesa a Fannin Shari’a a jami’ar Howard yace kudurin nada muhimmanci, saboda yana nuni da matakin koli da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka wajen amincewa da bautar da mutane a ketaren tekun Atlantika a matsayin cin zarafin dan adam, da kuma kira da a biya diyya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya shaidawa babban taron Majalisar cewa ana bukatar sauran kasashe su dauki mataki don fuskantar rashin adalcin da aka tafka a baya. Kasar Netherlands har yanzu ita ce kasa daya tilo a Turai da ta bayar da hakuri kan rawar da ta taka a bautar da mutane.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako
Next Post: Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA

Karin Labarai Masu Alaka

Zamu Tarwatsa Cibiyoyin Makamashi Da Cibiyoyin Mai Din Iran Amurka
Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kasar Nijar Afrika
An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami Najeriya
  • Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa Labarai
  • ‘Yan Kasar Venuzuela Zasu Fara Komawa Gida Amurka
  • An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
  • Amurka Ta Bada Tabbacin Baiwa Ukraine Tsaron Na Shekaru 15 Amurka
  • Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.