Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Farashin Mai Yana Cigaba Da Karuwa
Published: March 31, 2026 at 8:54 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ahalinda ake ciki kuma farashin mai mai daraja da ake kira Brent yayi tashin gwaron zabbi ranar talata, bayan wani sabon hari da Iran ta kai kan jirgin ruwa mai dakon mai a gabas ta tsakiya, da kuma gargadin da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayar cewa Washington zata zafafa kai hare hare muddin Farisa bata cimma yarjejeniya ba, hakan yasa farashin mai ya culla sama.

Danyen mai na Brent ya karu da dala 6 da centi 23, zuwa dala 119 kan ko wace ganga da misalin karfe 12 saura minti 25 agogon Amurka misalin hudu saura minti 25 agogon GMT, biyar saura 25 agogon Najeriya da Nijar, wadda yake nuna farashin man ya tashi da kashi 64 cikin dari cikin watan Maris, kamar yadda alkaluma suka nuna, tun shekara ta 1988, yayinda mai da ake kira West Texas, ya karu da kashi 56 cikin dari, rabon farashin ya kai haka tun shekara ta 2020.

A wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gudanar ya nuna mai da kasashe da suke cikin Kungiyar OPEC suke hakowa yayi kasa da kamar ganga milyan 7.3 a ko wace rana, daga wata zuwa wata, zuwa ganga milyan 21 kusan da rabi ako wace rana, wannan shine mai mafi karanci da kasashe da suke cikin Kungiyar suka samarwa tun lokacin da annobar Covid 19 ta tsaida harkoki a duniya.

A karon farko cikin shekaru hudu, Amurka zata saidawa Girka mai, yayinda matatun mai suke neman wata kafar samun mai sakamakon yakin da ake yi a gabas ta tsakiya.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon
Next Post: Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon

Karin Labarai Masu Alaka

Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
An Kashe Sojojin Bangladesh A Kasar Sudan Tsaro
Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • Bassirou: Tawagar Senegal Zasu Samu Kyautar Kudi Da Filaye Sakamakon Nasarar Da sukayi AFCON 2025 Wasanni
  • Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.