Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo
Published: April 6, 2026 at 1:58 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), sun kai samame a wata babbar ma’ajiyar miyagun kwayoyi a jihar Edo, inda suka kwace kilogram 1,378 na tabar wiwi da ake zargin an ɓoye, tare da kama wani da ake zargi da hannu a lamarin.

Kwamandan NDLEA a jihar Edo, Dr. Mitchell Ofoyeju, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Benin, yana mai cewa an gudanar da samamen ne a garin Igbanke da ke karamar hukumar Orhionmwon, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Ofoyeju ya ce samamen ya kai ga kwato buhun huna 125 na busasshen ganye da ake zargin nau’in tabar wiwi ce ta skunk.

A cewarsa, an kama wani mutum mai shekaru 37 mai suna Roland Owie dangane da wannan kamen.

Kwamandan ya bayyana wannan nasara a matsayin gagarumar ci gaba a kokarin hukumar na dakile hanyoyin samar da miyagun kwayoyi da yaɗa su.

Afrika, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Bola Tinubu Ya Amince Da Inganta Wutan Lantarki A Kasar
Next Post: Iran Zata Kawo Karshen Yaki Da Isra’ila Da Amurka

Karin Labarai Masu Alaka

Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gombe Ta Ƙarfafa Ilimin Almajirai Da Tsangaya Don Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Afrika
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda Najeriya
  • Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya Sauran Duniya
  • Karamar Sallah: Hukumar Kashe Gobara A Gombe Ta Kuduri Aniyar Kare Al’umma Afrika
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.