Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila
Published: April 9, 2026 at 9:28 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasar Iran ta yi barazanar kai hare-haren ramuwar gayya a kan Isra’ila wadda ta yi luguden wuta babu kaukautawa jiya laraba a kan Lebanon, in da ta kashe daruruwan mutane.

Iran ta ce a irin wannan yanayi, babu wata fa’ida ta yin tattanawar kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin da Amurka.

Wannan kashedin da ya fito ta bakin jagoran masu shawara na kasar Iran, wato kakakin majalisar dokoki Mohammed Bager Qalibaf, ya nuna zaman rashin sanin tabbas da ake ci gaba da shi a yankin a bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana a ranar talata.

Bangarorin biyu sun bayyana manufofin kishiyoyin juna game da shawarwarin neman zaman lafiyar da ake shirin farawa ranar asabar. Ba a ma san ko tsagaita wutar zata dore har zuwa lokacin da za a fara tattaunawar ba.

Qalibaf ya ce tuni kasar bani Ira’ila ta karya wasu daga cikin ka’idojin tsagaita wutar ta hanyar zafafa hare-hare a kan ‘yan Hezbollah masu goyon bayan Iran a Lebanon, a yayin da ita ma Amurka ta keta ka’idojin ta hanyar nacewa a kan lallai Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya.

Ya fada cikin wata sanarwa cewa a irin wannan yanayi, babu wata fa’ida ga tsagaita wuta ko yin shawarwari.

Amurka da Isra’ila sun ce wannan tsagaita wuta ba ta shafi abubuwan da suke faruwa a Lebanon ba, har ma firayim minista Benjamin Netanyahu yayi alwashin ci gaba da kai hare-hare.

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, wanda zai jagoranci tawagar mashawartan Amurka ya fadawa ‘yan jarida a Budapest cewa yana tsammanin (ran ta zaci cewa tsagaita wutar ta hada har da Lebanon ne, amma abin ba haka yake ba.

Duk da yake kowace daya daga cikin Amurka da Iran ta yi ikirarin samun nasara a yakin da aka gwabza na makonni 5, har yanzu ba a warware ko daya daga cikin muhimman batutuwan da suka takaddamar a kai ba. Kowaccensu ta dage a kan cimma muradunta a yarjejeniyar da zata shata alkiblar yanayin gabas ta tsakiya na shekaru masu yawa.

Hukumar tsaron fararen hula ta Lebanon ta ce Isra’ila ta kashe mutane 254 a hare-haren da ta kai cikin kasar jiya laraba. An kashe mafi yawa a Beirut babban birnin kasar inda mutane 91 suka mutu.

Ita ma Iran an ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin mai a kasashen yankin Gulf, ciki har da wani bututun mai na Saudiyya da ake amfani da shi wajen kaucewa mashigin ruwan Hormuz da Iran ta garkame. Kuwait da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa duk sun bada rahotannin hare-haren makamai masu linzami da jiragen drone.

Har yanzu mashigin ruwan na Hormuz yana rufe ga jiragen ruwan da ba su karbi takardar izinin shigewa ba. Masu safarar jiragen ruwa sun ce su na bukatar samun cikakken bayani kafin su fara zirga zirga. Wasu alkaluman zirga zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa jiragen ruwa biyu dauke da tutar Girka da wasu biyu dauke da tutar kasar China sun shige ta mashigin ruwan daga safiyar laraba zuwa yanzu.

A wasu sakonnin da yayi ta rubutawa a kafar sada zumunci, shugaba Trump ya ayyana kafa sabon harajin fito na kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin duk wata kasar da ta taimaka ma Iran da makamai, koda yake doka ba ta ba shi ikon yin hakan ba.

Dubban jama’a sun fantsama kan titunan kasar Iran cikin dare suna murna dauke da tutocin kasar, yayin da suke kona tutocin Amurka da Isra’ila.

Sai dai kuma wasu daga cikinsu sun bayyana shakkun ko tsagaita wutar zata dore, wasu na cewa zai yi wuya kasar Isra’ila ta kyale a cimma wani abu ta hanyar diflomasiyya, kuma shugaban Amurka Trump na iya waye gari ya ce ya canja ra’ayinsa.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara
Next Post: Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Bata Da Kiyayya Tsakaninta Da Amurkawa Afrika
Jagoran Kasar Iran Yace Basa Bukatar Tallafin Kasar Amurka Afrika
‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
  • An Kama Maharan Bom Din Maiduguri Tsaro
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Hare Hare Daban Daban A Najeriya Najeriya
  • Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika
  • Shirin Dare 26.11.2025 Rediyo
  • Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.