Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere
Published: April 20, 2026 at 2:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Al’ummar yankin Mushere dake karamar hukumar Bokkos a jihar Filato sun bukaci gwamnatin jihar da tabi matakan da dokar kasa da ta ayyana, waje dawo musu da babban hakiminsu da ta Sauke daga sarauta.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne gwamnatin jihar Filato ta tumbuke babban hakimin yankin Mushere a karamar hukumar Bakkos a jihar Filato, Dakta Julius Dibilang, lamarin da ya janyo zanga-zanga da matan yankin suka yi tsirara.

Shugaban kungiyar raya al’ummar Mushere, Duwaf Bosco yace al’ummar yankin basu fahimci hujjar da gwamnati ta bayar na cire sarkin nasu ba.

Yankin na Mushere, inda tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye ya fito, yayi shekaru bakwai babu hakimi, tun bayan rasuwar tsohon hakimin a shekarar dubu biyu da goma sha takwas, kafin a watan satumban bara, gwamnatin jihar ta nada Dakta Julius Dibilang a matsayin babban hakimin yankin.

Daya daga cikin matan da suka yi zanga-zanga kan cire sarkin tace yanzu sun kasance ba jagora, don haka zasu fuskanci matsaloli da dama.

To sai dai a bangaren gwamnati, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa sun sami hakimin da laifin da kotu ta yanke masa hukunci da bai bayyana ba har sai bayan da aka bashi takarda.

Gwamnan ya kara da cewa, bayan sun sami shaidu masu gamsarwa daga wadanda suka yi korafin nada sarkin, ya zamo dole gwamnati ta janye takardar amincewa da sarautar, saboda doka ta haramta wa duk wanda kotu ta same shi da laifi rike ko wani irin mukami, har sai kotun ta warware hukuncin.

A halin da ake ciki dai, cire hakimin na Mushere ya janyo rarrabuwar kawunan al’ummar yankin, wanda wassu bayanai ke nuni da cewa bisa al’ada, ba zai yiwu a sake zaben wani sarki ba, har sai wannan sarkin ya bar duniya, yayinda wassu ke cewa za’a iya zaben wani hakimin ya maye gurbinsa.

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/AUD-20260420-WA0101.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero
Next Post: An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika
Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda Najeriya
Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika
  • Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
  • Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
  • China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Labarai
  • Wike: Bazamuyi Sake Fubara Ya Sake Samun Nasara Ba Najeriya
  • Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
  • An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.