Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro Afrika
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN Afrika
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira Afrika
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe Afrika
  • An Horar Da Mata Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Gombe Afrika

Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa
Published: April 22, 2026 at 8:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

​Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Ibrahim Jibrin, ya ƙara faɗaɗa gagarumin shirinsa na tallafa wa al’umma, inda ya raba motoci 47 da kuma babura guda 282 ga mazaɓarsa ta Kano ta Arewa.

​Wannan tallafi, wanda aka raba wa rukunonin mutane daban-daban a birnin Kano ranar Laraba, na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Sanatan na ganin ya inganta rayuwar mutanen da yake wakilta.

Cikin waɗanda suka ci gajiyar wannan tagomashi har da ​Shugabannin jam’iyyar APC da sakatarorinsu daga ƙananan hukumomi 13 na mazaɓar, ​Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Firamare (Headmasters’ Forum), ​Shugabannin makarantun sakandare (Principals’ Forum), ​Da sauran ƙungiyoyin al’umma daban-daban.

Mai Magana da Yawun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ismail Mudashir, ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin magance matsalar sufuri, inganta ayyukan ƙungiyoyin, da kuma ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin al’umma.

​Malam Salihu Sagir Takai, wanda shi ne Kodinetan Tsarin Renewed Hope a Jihar Kano, ya bayyana a wurin taron cewa wannan yunƙuri na Sanata Barau ya yi daidai da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta jin daɗin ‘yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, “Wannan ba shi ne karon farko da Sanatan yake yin irin wannan ba, kuma ba shi ne na ƙarshe ba.”

Sanata Barau, wanda Babban Jami’in Ma’aikatansa (Chief of Staff), Farfesa Muhammad Ibn Abdullah ya wakilta, ya ce babban burinsa shi ne fitar da mutane daga kangin talauci.

​Ya yi kira ga waɗanda suka amfana da kada su kuskura su sayar da waɗannan motoci da babura, maimakon haka su yi amfani da su ta hanyar da za ta riƙa kawo musu kudin shiga da kuma taimaka wa ayyukansu na yau da kullum.

​Wannan dai na ɗaya daga cikin jerin shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki da Sanatan ya tsara domin mazaɓarsa ta Kano ta Arewa da ma jihar baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi Afrika
Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya
Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH Afrika
Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
Kasar Habasha Da Turkiyya Sun Kulla Yarjejeniyar Makamashi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe
  • Tinubu Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Sake Zaɓensa A 2027

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • PDP Zata Karbi Mulki 2027 Inji Shugabannin Jam’iyar Siyasa
  • Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
  • Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
  • ‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
  • Boko Haram Sun Dauke Kansiloli A Borno Tsaro
  • Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • Kasar Mauritius Zata Rage Amfani Da Makamashi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.