Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya
Published: April 22, 2026 at 8:42 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da kudi naira biliyan 17 domin gudanar da wani babban shiri na samar da ci gaba a matakin mazabu (Wards) da ke faɗin ƙasar nan.

​Wannan tallafi, wanda aka yi wa laƙabi da “Community-Based National Social Action Fund”, an kafa shi ne domin taba rayuwar talakawa kai-tsaye a dukkanin mazabu 8,804 na Najeriya, ta hanyar ba su damar gudanar da ayyukan da suka fi damunsu a yankunansu.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta fitar ranar Laraba, wadda mataimakin daraktan yaɗa labarai, Ado Bako ya sanya wa hannu, an bayyana cewa kowace mazaba za ta haɗa gwiwa ne da ƙungiyoyin sa-kai na cikin gida (CBOs) domin gano ayyukan da suka fi buƙata.

​Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa wannan sabon salo ne na mika mulki ga talakawa. Ya ce, “Wannan tsari ya sanya al’umma a gaba wajen neman ci gaba. Ta hanyar barin kowace mazaba ta zaɓi abin da ya fi damunta, muna buɗe hanyoyin samar da maslaha da za su inganta rayuwa da kuma ayyukan gwamnati a inda aka fi buƙata.”

Sanarwar ta nuna cewa za a kashe kuɗaɗen ne a fannonin da suka haɗa da​Samar da abinci mai gina jiki ga al’umma, ​Samar da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya, ​Gyaran makarantu, asibitoci, da samar da tsarin tsaftar muhalli.

​An tsara cewa za a fara aiwatar da wannan shiri ne daga ranar 1 ga watan Maris, 2026 zuwa watan Disambar 2026, inda Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa za su kula da asusun da aka ware wa shirin.

A wani labarin kuma mai alaƙa da wannan, Shugaba Tinubu ya amince da ɗaga matsayin Cibiyar Horar da Masu Maganin Kanjamau da Kuturta ta Ƙasa (NTBLTC) da ke Zariya, zuwa matsayin Babbar Cibiyar Bincike da Kula Lafiyar Jama’a da Cututtuka Masu Yaduwa (National Institute of Public Health and Infectious Diseases).

​Wannan mataki na nufin mayar da cibiyar ta Zariya ta zama tungar bincike, horarwa, da kuma shirin taryar duk wata annoba ko barazanar cututtuka da ka iya ɓallowa a ƙasar nan.

Afrika, Labarai, Najeriya, Sana'o'i, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa
Next Post: Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya

Karin Labarai Masu Alaka

Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
An Garkame Dan Majalisa Watannin Takwas A Kasar Tunisiya Afrika
Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma Afrika
An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
  • Jam’iyar NNPP: Abba Kabir Yusuf Yaci Amanar Mu Siyasa
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
  • Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
  • Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya Labarai
  • Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.