Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna
Published: April 24, 2026 at 4:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tun bayan da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ayyana Sanata Aliyu Wadada a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi a kujerar gwamna, kasancewar ya kammala shekaru takwas da doka ta kayyade, al’ummar jihar ke ta cecekuce kan dacewa da rashin dacewar zabin na gwamna.

Aliyu Wadada wanda Sanata ne a majalisar dattawan Najeriya, ya ci zabe ne a karkashin jami’iyyar SDP, bayan ya shanza sheka daga jami’iyyar APC, kafin daga bisani ya sake komawa jami’iyyar ta APC.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Honarabul Aliyu Bello yace ba abin tashin hankali bane don gwamna ya fadi ra’ayinsa.

Shiko Dadda’u Mamuda dan jami’iyyar APC ne a jihar Nasarawa, ya bayyana rashin amincewa da matakin gwamnan na fidda Sanata Aliyu Wadada a matsayin dan takara.

A gefe guda kuwa, mataimaki na musamman ga Sanata Aliyu Wadada a kan harkokin watsa labarai, Musa Umar Aboki yace gwamnan bai yi zaben tumun dare ba, saboda Aliyu Wadada masanin harkokin siyasa ne kuma yana da tarin magoya baya.

Abin jira a gani shine yadda zata kaya kafin zaben dubu biyu da ishirin da bakwai.

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/CECE-KUCE-KAN-TSAYAR-DA-DAN-TAKARA-A-APC-JIHAR-NASARAWA.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu
Next Post: Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru

Karin Labarai Masu Alaka

Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta Afrika
Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
  • Iran Da Amurka Zasu Cimma Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
  • Kasar Ghana Ta Umarci ‘Yan Kasar Su Daina Zuba Jari A Kasashen Waje Afrika
  • Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
  • Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe Najeriya
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.