Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe
Published: April 29, 2026 at 1:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A yau Laraba matasan gidan Professor Isa Ali Pantami da suka hada mishi fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin siyan form din tsayawa takara sun cika burinsu na siyan form din.

Idan baku manta ba a ranar Jumma’a da ta gabata Matasan da Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, yayi silar taimakon rayuwarsu da masoyanshi suka kudiri aniyar saya mishi form din tsayawa takarar Gwamnan jihar Gombe a kokarin matasan na maida halaccin taimakonsu da Professor Isa Ali Pantami yayi a rayuwarsu.

Wannan dalilin yasa matasan suka kafa kwamitin gaggawa a tsakaninsu ba tare da wani ya saka su ba, inda a cikin kwanaki biyu kacal suka hada fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin da ya zarce na iya siyan form din.

Dukkannin mutanen da suka bada gudummuwarsu babu wanda aka saka ya bayar kowa radin kanshi

Wannan yake kara nunawa duniya cewa Majidadin Daular Usmaniyya ya kafa matasa da ayyukan yi a damar da ya samu.

A yau Laraba wakilan wasu daga cikin matasan suka je inda ake saida form din, suka cika burinsu na siyawa Malam Isa Ali Pantami form din kamar yadda suka kudiri aniya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027
Next Post: Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark

Karin Labarai Masu Alaka

Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
Fitaccen Dan Jarida a Sokoto Surajo Dalhatu Sifawa Ya Rasu Najeriya
NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati Afrika
Rasha Ta Gargadi Amurka Da Isra’ila Kan Harin Iran Afrika
Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
  • Shugaban Amurka Zai Sake Gine Gaza Amurka
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
  • Newcastle Na Dab Da Kammala Yarjejeniyar Daukar Højbjerg Daga Marseille Kan €15m Wasanni
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u Afrika
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.