Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani
Published: May 20, 2026 at 8:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sanata Sa’idu Ahmed Alkali ya sanar da kauracewa shiga zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Gombe ƙarƙashin jam’iyyar APC, wanda aka shirya gudanarwa ranar Alhamis 21 ga watan Mayun 2026.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Umar Alkali Jibrin ya fitar, Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya bayyana a matsayin rashin gaskiya da kuma take dokokin zaɓe a zaɓukan fidda gwani na kujerun Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa da aka gudanar a wasu sassan jihar.

Sanarwar ta ce zaɓukan da aka gudanar a mazabun Gombe, Kwami da Funakaye da Billiri da Balanga, da kuma Yankin Sanatan Gombe ta Tsakiya, sun kasance cike da maguɗi, rashin bayyana gaskiya da kuma rashin bin ƙa’idojin da Dokar Zaɓe ta 2026 da kundin tsarin jam’iyyar APC suka tanada.

Sanata Alkali Wanda shine Tsohon Ministan Sufurin Najeriya, ya bayyana cewa an sanar da sakamakon wasu zaɓukan ba tare da gudanar da sahihin zaɓe ba, inda ya ce an gudanar da tsarin ba tare da kayan zaɓe, jami’an gudanarwa da masu sanya ido yadda ya kamata ba.

Ya ƙara da cewa waɗannan matsaloli sun sa jama’a da masu ruwa da tsaki suka rasa amincewa da tsarin zaɓukan fidda gwani a jihar.

Sai dai duk da kauracewar tasa, Sanata Alkali ya jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC tare da bayyana aniyarsa ta ci gaba da mara wa jam’iyyar baya domin samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.

Haka kuma ya yi kira ga shugabannin APC na ƙasa da su soke zaɓukan da aka gudanar a yankunan da ake korafi a kansu, tare da kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Sanata Alkali ya kuma gode wa magoya bayansa da al’ummar jihar Gombe bisa haƙuri da natsuwar da suke nunawa duk da halin da ake ciki.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara
Next Post: Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
Dakarun Sakai A Kasar Sudan Sun Kashe Mutane 28 A Wani Farmaki Afrika
Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
Paparoma Leo: Zai Kai Ziyara Ƙasar Angola Labarai
NANPAN Ta Wayar Da Al’umma Kan Amfanin Shayar Da Jarirai Nono Kaɗai Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
  • ‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
  • Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
  • Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026 Shirye-Shirye
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran Amurka
  • Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.