Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki
Published: May 21, 2026 at 2:18 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da ƙasar Poland wajen inganta harkokin tsaron cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi Mataimakin Firaministan Poland, Krzysztof Gawkowski, a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Tunji-Ojo ya ce Najeriya na da burin anfani da ƙwarewar Poland wajen kula da iyakoki da kuma dabarun tsaron cikin gida da suka tabbatar da nasara a ƙasar.

Ya ce gwamnatin Najeriya na sa ran yin haɗin gwiwa da Poland musamman a fannoni kamar horas da jami’ai, amfani da fasaha, tsaron yanar gizo da sauran muhimman fannoni.

“Mun yi imani cewa haɗin kai da koyo daga juna ne hanya mafi dacewa wajen rage rauninmu tare da ƙarfafa bangarorin da muke da ƙwarewa,” in ji shi.

Ministan ya tabbatar wa baƙin cewa ziyarar ba za ta zama ta al’ada kawai ba, domin za ta zama tubalin da za a gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa ana shirye-shiryen kai ziyara ƙasar Poland domin ƙara zurfafa tattaunawa da gwamnatin ƙasar da kuma ɓangaren kasuwanci masu alaƙa da ma’aikatar harkokin cikin gida.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na nuna cewa gwamnati na fahimtar hanyoyin gina tattalin arziki mai ƙarfi.

A nasa jawabin, Mataimakin Firaministan Poland, wanda kuma shi ne Ministan Harkokin Dijital na ƙasar, Krzysztof Gawkowski, ya ce Najeriya ƙasa ce mai tarin albarkatun tattalin arziki, yawan jama’a da kuma damar ci gaban fasaha.

Ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa wajen gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Gawkowski ya ce Poland a shirye take ta taimaka wa Najeriya ta hanyar ƙwarewarta a fannoni kamar kirkire-kirkire, fasahar zamani, gina ababen more rayuwa da kuma sabbin dabarun fasaha.

Haka kuma ya bayyana fatan ganin Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya ya kai ziyara Poland domin ƙara ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani
Next Post: Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Diphtheria: Mutane 23 Sun Mutu A Jihar Filato Afrika
Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
  • Babu Dabbar Da Zata Sake Shiga Amurka Daga Mexico! Amurka
  • Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
  • Tsofin Ma’aikatan Gwamnati Sunyi Zanga Zanga A Jihar Neja Labarai
  • Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.