Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu
Published: May 24, 2026 at 6:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An shiga jimami a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood bayan rasuwar tsohuwar jarumar fina-finai, Wasika Ismail.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu bayan fama da rashin lafiya, lamarin da ya jawo alhini da ɗimuwa tsakanin ‘yan uwa, abokan aiki da masoyanta a faɗin ƙasar nan.

Marigayiya Wasika Ismail ta kasance ɗaya daga cikin fitattun tsoffin jaruman Kannywood da suka taka rawa wajen bunƙasa masana’antar fina-finan Hausa tun a shekarun baya. Ta shahara wajen fitowa a fina-finai masu ɗauke da darussa da al’adun Hausawa, inda ta samu karɓuwa a zukatan masu kallo saboda ƙwarewarta da salon gudanar da rawa.

Mutane da dama daga cikin ‘yan masana’antar Kannywood sun bayyana alhininsu kan rasuwar tata, suna masu bayyana ta a matsayin mace mai mutunci, biyayya da son taimakon jama’a.

Wasu daga cikin abokan aikinta sun bayyana cewa rasuwarta babban gibi ne ga masana’antar, musamman ganin yadda ta bayar da gudunmawa wajen haɓaka harkar fina-finan Hausa da kuma tarbiyyar matasa ta hanyar shirye-shiryen da take fitowa a ciki.

Masoya da mabiyanta sun ci gaba da bayyana alhini a shafukan sada zumunta, inda suke addu’ar Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta tare da ba iyalanta da ‘yan uwanta haƙurin jure wannan babban rashi.

An gudanar da jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci tare da halartar ‘yan uwa, abokai da wasu daga cikin fitattun jaruman Kannywood.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa
Next Post: Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11

Karin Labarai Masu Alaka

Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas Labarai
Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa Afrika
Boko Haram Ta Kai Hari Maiduguri Cikin Dare Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen Afrika
  • Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
  • CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna Afrika
  • Rikicin Aure: Albani Agege Ya Zargi Sheikh Gumi Da Boye Matarsa ‘Yar Morocco Afrika
  • Da Arzikin Mu: Bamu Ba Bautawa Turawan Yamma Afrika
  • Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali Afrika
  • Messi Da Cristiano Suna Da Tasiri A Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Wasanni
  • Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.