Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai
Published: June 1, 2026 at 4:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Alhazai ta Kasar Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa za a fara jigilar alhazan Najeriya zuwa gida daga ranar 3 ga watan Yuni, tare da yin kira ga alhazai da su bi ka’idojin tafiye-tafiye domin kauce wa jinkiri.

Shugaban Sashen Ayyukan Jiragen Sama na hukumar, Alhaji Habib Bello, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Makkah.

Ya ce jadawalin tashin jiragen dawowa yana karkashin kamfanonin jiragen sama ne tare da amincewar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA), wadda ke ware lokutan tashin jirage ga kamfanoni daban-daban.

A cewar sa, kamfanin Max Air zai fara jigilar alhazan Jihar Nasarawa daga ranar 3 ga Yuni, yayin da Flynas da Air Peace za su fara jigilar alhazan jihohin Ogun da Oyo daga ranar 4 ga Yuni.

Bello ya ce an tanadi dokar daukar jakunkuna biyu masu nauyin kilo 23 kowanne da kuma jakar hannu mai nauyin kilo 8, yana mai gargadin cewa rashin bin wannan ka’ida na iya haifar da jinkirin tashi ko hana mahajjaci shiga jirgin.

Ya kuma bukaci alhazai da jami’an jihohi su sanar da hukumomi akalla sa’o’i 48 kafin ranar tafiyarsu domin saukaka shirye-shiryen fitar da fasfo, jigilar kaya da sauran muhimman matakai.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Fasfo na NAHCON a Makkah, Alhaji Abdurrahman Mohammed, ya ce an kammala matakin farko na aikin Hajjin bana cikin nasara, kuma an fara shirye-shiryen fitar da fasfofin alhazan da za su koma gida.

Ya bayyana cewa ana ajiye fasfofin alhazai ne domin kare su daga bacewa ko lalacewa, tare da tabbatar da saukin gudanar da harkokin tafiya.

Mohammed ya ce duk mahajjacin da ke shirin tafiya ya kamata ya gabatar da bayanansa akalla sa’o’i 48 kafin tashinsa domin a samu saukin fitar da fasfonsa da kuma shirya masa tafiya.

Ya tabbatar da cewa akwai matakan da aka tanada domin gano fasfofin da suka bace, yayin da za a samar da Takardar Tafiya ta Gaggawa (ETC) ga duk wanda ba a samu fasfonsa ba.

Jami’an biyu sun yi kira ga alhazai da jami’an kula da su da su ba da hadin kai domin tabbatar da cewa aikin dawo da alhazan Najeriya ya gudana cikin sauki da nasara.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Next Post: Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa Labarai
Iran Ta Rufe Sararin Samaniyar Ta Labarai
Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis Afrika
  • Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Agajin Izalar Jos Sunyi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.