Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

NAHCON Ta Yaba da Nasarar Hajjin 2026, Ta Fara Shirin Hajjin Shekara Mai Zuwa
Published: June 23, 2026 at 9:06 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: June 23, 2026

Hukumar Alhazai ta Najeriya wato (NAHCON) ta sanar da kammala jigilar alhazan Najeriya daga Kasar Saudiyya bayan gudanar da aikin Hajjin bana na 2026, inda ake sa ran jirgi na karshe da ke dauke da alhazan Jihar Zamfara zai sauka a Najeriya a yau, 23 ga Yuni, 2026.

Da wannan ne aka rufe shafin ayyukan Hajjin 2026 gaba daya, bayan nasarar jigilar dubban alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki da kuma dawo da su gida lafiya.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa akwai alhazai ’yan Najeriya 12 da ke ci gaba da karbar magani a wasu asibitoci daban-daban da ke Saudiyya sakamakon matsalolin lafiya.

NAHCON ta ce tana sa ido sosai kan halin da suke ciki tare da shirya yadda za a dawo da su Najeriya cikin aminci da zarar an sallame su daga asibiti.

Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya mika godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da aka samu a aikin Hajjin bana. Haka kuma ya yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, bisa goyon baya da hadin kan da suka bayar wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin.

Hukumar ta kuma gode wa Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi, kamfanonin yawon Hajji masu lasisi, masu samar da ayyuka, kamfanonin jiragen sama, ma’aikatan lafiya, jami’an tsaro, kafafen yada labarai da kuma alhazan Najeriya saboda gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da aikin.

NAHCON ta amince cewa kamar yadda ake samu a manyan ayyuka irin wannan, an fuskanci wasu kalubale a yayin gudanar da Hajjin. Sai dai ta ce an dauki darussa masu muhimmanci daga abubuwan da suka faru, kuma za a yi amfani da su wajen inganta ayyukan Hajji a nan gaba.

A wani bangare kuma, hukumar ta sanar da fara shirye-shiryen Hajjin shekarar 1448H/2027 tun kafin kammala dukkan ayyukan bana. A cewar hukumar, an sanar da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar Hajji ta wata takarda mai dauke da kwanan watan 15 ga Yuni, 2026, mai taken “Fara Shirye-shiryen Hajjin 1448H/2027” wadda Sakataren Hukumar, Dakta Mustapha Muhammad Ali, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban NAHCON.

Saboda haka, hukumar ta umarci Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da kamfanonin yawon Hajji masu zaman kansu da su fara shirye-shiryensu nan take bisa tsarin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta gindaya domin Hajjin shekarar 2027.

NAHCON ta ce daukar matakan tun da wuri zai taimaka wajen kara inganta shirye-shiryen Hajji da kuma tabbatar da samun nasara mafi girma a shekarun da ke tafe.

Amurka, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APM A Bauchi Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan ₦21 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bara Da Shira
Next Post: Shugaban Miyetti Allah Zai Fuskanci Shari’a Kan Zargin Badakalar Kuɗi da Ta’addanci

Karin Labarai Masu Alaka

NNPC Da Wasu Kamfanoni Sunyi Yarjejeniyar Iskar Gas Najeriya
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jama’ar Jos Ta Arewa Su Rika Bin Doka Afrika
Harin Da Israela Ta Kai Gaza Yayi Ajalin Mutane 27 Da Yara Uku Labarai
Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko Afrika
‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
  • Jami’an Shige Da Ficen Amurka Sun Harbe Wani Har Lahira Amurka
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Iran Tayi Allah Wadai Da Kai Hari Cibiyar Pars Afrika
  • NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Afrika
  • Prime Ministar Italiya Ta Ziyarci Saudi Arabia Afrika
  • Rasha Takai Sabbin Hare-Hare Akan Wasu Biranen Ukraine Tsaro
  • Manoma Suna Fuskantar Barazanar Karyewa A Kasar Ghana Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.