Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika

PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe
Published: June 30, 2026 at 12:49 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen jihar Gombe ta bayyana damuwa kan wasu matakan da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta ɗauka a baya-bayan nan, inda ta zargi gwamnatin da karya ƙa’idodin dimokuraɗiyya da kuma tauye haƙƙin wasu ‘yan jihar.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na jam’iyyar a jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku ya sanya wa hannu, PDP ta ce rushe-rushen kadarori da gine-gine da gwamnatin jihar ke aiwatarwa ya haifar da damuwa da rashin jin daɗi a tsakanin al’umma.

Jam’iyyar ta kuma nuna rashin jin daɗinta kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta wanda ke nuna Gwamna Inuwa Yahaya yana furta kalamai da wasu ke ganin ba su dace da matsayin gwamna ba.

PDP ta ce dukkan ‘yan jihar na da haƙƙin samun girmamawa da kariya ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin siyasa ba.

Haka kuma, PDP ta yi Allah-wadai da abin da ta kira korar kamfanin Gombawa Motors daga Dankwambo Modern Mega Motor Park. Jam’iyyar ta yi zargin cewa matakin yana da alaƙa da ra’ayin siyasar wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sufurin, lamarin da ta ce bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.

A cewar jam’iyyar, an gina tashar Dankwambo Modern Mega Motor Park ne da kuɗaɗen jama’a domin amfanin kowa da kowa, don haka bai kamata a hana wani mai gudanar da harkokin sufuri amfani da ita saboda dalilan siyasa ba.

Dangane da zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar, PDP ta ce zaɓen bai kasance cikin adalci, gaskiya da sahihanci ba.

Jam’iyyar ta bayyana cewa tsarin zaɓen bai bai wa jam’iyyun adawa damar yin gogayya cikin adalci ba.

PDP ta kuma ce rahotannin da suka nuna rashin isassun kayan zaɓe da akwatunan zaɓe a wasu rumfunan zaɓe sun ƙara jefa shakku kan sahihancin zaɓen.

Jam’iyyar ta jaddada cewa ta kaurace wa shiga zaɓen ne saboda abin da ta bayyana a matsayin rashin amincewa da tsarin gudanar da zaɓen.

A ƙarshe, PDP ta yi kira ga gwamnatin Jihar Gombe da ta mutunta ƙa’idodin dimokuraɗiyya, ta kare haƙƙoƙin kundin tsarin mulkin ‘yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa ba a yi amfani da cibiyoyin gwamnati wajen takura wa abokan hamayyar siyasa ba.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC
Next Post: NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika
Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai
An Zargi Shugaba Trump Da Kalaman Da Basu Dace Ba Afrika
Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko Afrika
  • Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya Labarai
  • Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Gyara Harkokin Cinikayya Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
  • Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya Farashin Mai Ya Karu Labarai
  • Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.