Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani
Published: July 4, 2026 at 4:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ofishin Mai Bai wa Gwamnan jihar Bauchi Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mukhtari Gidado, Jarman Alkaleri, ya shirya taron horaswa na kwanaki uku ga ‘yan jaridar Gidan Gwamnatin jihar Bauchi a jihar Gombe.

An gudanar da taron ne daga 1 zuwa 3 ga Yulin 2026 a Flourish Hotels Ltd., Gombe, inda aka mayar da hankali kan haɓaka ƙwarewar mahalarta a fannin fasahar sadarwar zamani da kuma ƙarfafa bin ƙa’idojin ɗa’a a aikin jarida.

Taron, mai taken “Ƙarfafa Ƙwarewar ‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi ta Hanyar Horar da Su kan Fasahar Zamani da Kayan Aikin Jarida Masu Bin Ɗa’a domin Inganta Isar da Manufofin Gwamnati da Gina Amincewar Jama’a,” ya bai wa mahalarta ilimi da sabbin dabarun aikin jarida, waɗanda za su taimaka musu wajen isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati cikin inganci tare da ƙarfafa amincewar al’umma.

A jawabin maraba, Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alhaji Mukhtari Gidado, ya jaddada aniyar Gwamnatin Jihar Bauchi na ci gaba da bunƙasa ƙwarewar ‘yan jarida ta hanyar shirya irin waɗannan tarukan horaswa akai-akai domin su dace da sauye-sauyen da ake samu a harkar yaɗa labarai.

Shi ma da yake jawabi a madadin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi), Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Dr. Usman Shehu Usman, ya taya mahalartan murnar samun damar halartar taron, tare da buƙatar su yi amfani da ilimin da suka samu wajen ƙara ƙwarewa da inganta ayyukansu.

A nasa jawabin, Mataimaki na Musamman kan Sadarwa ga Gwamnan jihar Bauchi, kuma fitaccen ɗan jarida Alhaji Abdulwahab Muhammad, ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma mai matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa aikin yaɗa labaran gwamnati.

Ya kuma buƙaci mahalarta su yi amfani da ilimi da ƙwarewar da suka samu domin inganta ayyukansu da kuma tabbatar da ingantacciyar sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.

Haka kuma, taron ya bai wa mahalarta damar musayar ra’ayoyi, haɓaka ƙwarewarsu ta aiki, tare da tattauna sabbin hanyoyin amfani da fasahar zamani wajen inganta sadarwar gwamnati da jama’a.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran
Next Post: An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen

Karin Labarai Masu Alaka

An Garkame Dan Majalisa Watannin Takwas A Kasar Tunisiya Afrika
Gidauniyar Jalo Wali Ta Ƙaddamar Da Bada Audugar Mata A Gombe Afrika
Sakamakon Yakin Gabas Ta Tsakiya Kowacce Gangar Mai Ta Haura Dala 100 Afrika
Masu Hakar Ma’adanai 37 Sun Mutu A Jihar Filato Bidiyo
Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Sojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Kano Da Katsina Tsaro
  • Sakamakon Yakin Gabas Ta Tsakiya Kowacce Gangar Mai Ta Haura Dala 100 Afrika
  • Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF Wasanni
  • Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.