Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da haɗa baki wajen aikata laifi, yin barazanar garkuwa da mutum ta hanyar kira da saƙonnin waya ba tare da bayyana ainihin su ba, tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 30.
Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani mazaunin garin Jega, Alhaji Aminu Garba, ya kai rahoton cewa yana karɓar kiraye-kirayen waya masu ɗauke da barazanar yin garkuwa da shi idan har bai biya Naira miliyan 30 ba.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Muhammad Shafiu mai shekaru 21, Mansur Ibrahim mai shekaru 21, Aliyu Umar mai shekaru 25 da kuma Muhammad Suleiman mai shekaru 23.
Binciken farko ya nuna cewa mutane uku daga cikin waɗanda ake zargin sun sayi sabon layin waya, sannan suka riƙa kiran wanda abin ya shafa, inda ɗaya daga cikinsu ya canja murya domin ta yi kama da ta Bafullatani, da nufin tsoratar da wanda ake yi wa barazanar tare da ɓoye ainihin sa.
Binciken ya kuma gano cewa Muhammad Suleiman, wanda ake zargin abokin iyalan wanda aka yi wa barazanar ne, ya bayar da lambar wayarsa da wasu bayanan iyalansa, waɗanda aka yi amfani da su wajen aiwatar da wannan shiri.
Rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar gano tare da cafke waɗanda ake zargin a ƙauyukan Gumbin Kure da Gamjeji da ke Ƙaramar Hukumar Maiyama, lamarin da ya dakile shirin kafin a aiwatar da shi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya ba da umarnin zurfafa bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bisa tanadin doka.
Ya kuma jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu a laifukan garkuwa da mutane, karɓar kuɗin fansa ko makamantansu zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Rundunar ta buƙaci al’umma su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da kai rahoton duk wani kira ko motsi da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.


