Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Tinubu Ta Warware Basussukan Fansho Na Shekaru 18
Published: July 14, 2026 at 7:47 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta aiwatar da manyan sauye-sauye a fannin fansho cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ta kashe Naira biliyan 758 wajen biyan basussukan haƙƙoƙin fansho da suka taru tun daga shekarar 2007, tare da ƙara kuɗaɗen da masu ritaya ke karɓa a kowane wata.

Darakta Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Misis Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Talata.

A cewarta, matakin ya amfani kusan masu ritaya 957,045, tare da rage gibin biyan haƙƙoƙin fansho daga jinkirin watanni 21 zuwa yanayin da gwamnati ke da tanadin kuɗin biyan fansho na watanni 41 a gaba.

Ta ce jimillar kuɗaɗen da ke cikin tsarin fansho ta haura daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48 cikin shekaru biyu, abin da ta ce ya nuna ƙaruwar amincewar ma’aikata da tsarin, yayin da sabbin ma’aikata sama da 938,000 suka shiga tsarin fansho a wannan lokaci.

Omolola ta kuma bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da shirin Pension Boost 1.0, wanda ya ƙara jimillar kuɗin fansho da ake biya a kowane wata daga Naira biliyan 12.2 zuwa Naira biliyan 14.9.

Haka kuma, ta ce gwamnatin ta amince da ƙarin Naira 32,000 ga dukkan masu ritayar ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi ritaya kafin 29 ga Yulin 2024, domin daidaita kuɗin fanshonsu da sabon mafi ƙarancin albashi.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central
Next Post: Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
  • Boko Haram Ta Kai Hari Maiduguri Cikin Dare Afrika
  • An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai
  • Osun: Adeleke Ya Doke Oyebamiji, Ya Ci Gaba Da Rike Kujerar Gwamna Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.