Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027
Published: July 15, 2026 at 5:25 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da sake tsayar da Mataimakin Gwamna, Alhaji Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin abokin takararsa domin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.

Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna Yusuf ya bayyana matakin ne yayin wani taron dabarun siyasa da ya yi da masu riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya daga jihar Kano da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, wanda aka gudanar a masaukin gwamnatin jihar da ke Abuja.

Ya ce ya yanke shawarar sake zaɓen Murtala Garo ne bisa irin biyayya, jajircewa da ƙwazon da ya nuna wajen gudanar da aikinsa tun bayan hawansu mulki.

Gwamnan ya ce ya gamsu da yadda suke aiki tare, yana mai bayyana Mataimakin Gwamnan a matsayin mutum mai ƙwarewa, sadaukarwa da cikakken ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansa.

A cewarsa, “Ban taɓa nadamar zaɓen Garo a matsayin Mataimakina ba. Ya tabbatar da cewa shi ne ya dace da wannan matsayi, kuma ina da cikakken yaƙini da ƙwarewarsa.”

Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cikakken goyon bayansa ga Mataimakin Gwamnan, yana mai cewa gudummawar da yake bayarwa ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ci gaba mai ma’ana ga al’ummar Kano.

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya baya da su ci gaba da haɗa kai tare da mara wa gwamnati baya yayin da take ci gaba da aiwatar da manufofinta tare da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye
Next Post: Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe Kimiya
Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yeriman Ingila Ya Mayarwa Trump Martani Amurka
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi Afrika
  • Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Yayi Tashin Gwaron Zabi Afrika
  • Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya Afrika
  • Jami’an Shiga Da Fice A Afirka Ta Kudu Sun Tafka Badakalar Kudade Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.