Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe
Published: July 22, 2026 at 4:59 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a na yini guda kan wasu muhimman kudurorin dokoki guda biyu da ke da nufin inganta tsarin kula da muhalli da gandun daji a jihar.

Kudurorin da aka tattauna sun haɗa da kudurin soke Dokar Hukumar Kula da Tsabtace Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA) ta shekarar 2006, da kuma kudurin soke tare da sake kafa Dokar Gandun Daji ta shekarar 2026 domin samar da ingantaccen tsarin doka na zamani da zai tabbatar da dorewar kula da gandun daji da kare muhalli.

Da yake buɗe taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Rt. Hon. Abubakar Muhammad Luggerewo, ya yi maraba da mahalarta taron tare da jaddada muhimmancin samar da dokoki ta hanyar bai wa jama’a damar bayar da gudunmawa, yana mai cewa hakan ne zai taimaka wajen samar da dokokin da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

Shugaban Kwamitin Majalisar da ke kula da kudurorin, Hon. Musa Manaja Zambuk, wanda ya jagoranci zaman, ya ce majalisar ta himmatu wajen tabbatar da cewa sabbin dokokin za su dace da muradu da buƙatun al’ummar Jihar Gombe.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Mai Kula da Aikin ACReSAL, Ambasada Dakta Sani Adamu Jauro; Babban Sakataren Hukumar GOSEPA, Dakta Auwalu Baba Jada; Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Gombe kan Harkokin Muhalli da Kula da Yanayi, Alhaji Mu’azu Garba; Daraktan Gandun Daji, Alhaji Inuwa Ahmed Ba’agale; da Alhaji Abdu, Mataimakin Sakataren Kwamitin Gombe Goes Green (3G).

Taron ya kuma samu halartar wakilan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararru a fannin muhalli, da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka gabatar da shawarwari da bayanai kan tanade-tanaden kudurorin domin ƙara inganta su kafin amincewa da su.

Kwamitin Gombe Goes Green (3G) ya kasance cikin mahalarta taron, inda ya bayyana cewa duba da sabunta waɗannan dokoki wani muhimmin mataki ne wajen ƙarfafa kariyar muhalli, bunƙasa juriyar sauyin yanayi, da tabbatar da dorewar kula da albarkatun ƙasa a Jihar Gombe.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa sabbin kudurorin sun yi daidai da manufar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ta sabunta tsofaffin dokokin muhalli, ƙarfafa hukumomin da ke kula da harkokin muhalli, da kuma tabbatar da amfani da albarkatun ƙasa ta hanyar da za ta amfani al’ummomin yanzu da masu zuwa.

Sun kuma bayyana cewa idan aka amince da waɗannan dokoki, za su taimaka wajen samar da muhalli mai tsafta, kare gandun daji daga lalacewa, da kuma inganta ci gaba mai ɗorewa a fadin Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Mambobinta Su Marawa Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna Baya A Gombe
Next Post: Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo Najeriya
Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa Afrika
Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati Afrika
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Afrika
  • Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.