Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis
Published: July 26, 2026 at 2:20 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wani dan kasuwa mai shekaru 55, Onuigbo Ndubisi Chinedu, bisa zargin yunkurin fitar da kilo 3.3 na hodar iblis da aka boye a cikin kwali na kayan abinci da za a tura zuwa Birtaniya.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama mutumin ne bayan jami’an hukumar sun tare kayan a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, inda bincike ya gano shi ne jagoran wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar ta kuma kama wata ‘yar kasuwa mai shekaru 31, Emmanuella Chukwu-Edo, bayan kwace kilo 2.8 na wani nau’in tabar wiwi mai suna Loud da aka shigo da shi daga Amurka.

Hakazalika, NDLEA ta ce ta kwato kwayoyin maganin Tapentadol 250mg miliyan 2.24 da darajarsu ta haura Naira biliyan 2.2 daga wani kaya da ya fito daga Indiya.

A tashar jiragen ruwa ta Apapa kuwa, jami’an hukumar sun gano buhuna 4,777 na tabar wiwi nau’in Canadian Loud mai nauyin kilo 2,388.5 da darajarta ta zarce Naira biliyan 7.1, wadda aka boye cikin motoci uku a cikin kwantena.

A jihar Katsina, NDLEA ta kama wasu mutane biyu dauke da harsasai 396 na bindigogi, tare da mika su ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike.

A jihar Edo kuma, hukumar ta kwace kilo 1,286 na tabar wiwi da kilo 86 na irin ta, sannan ta kama wasu mutane biyu dauke da kilo 73 na tabar wiwi. NDLEA ta ce tana ci gaba da matsa kaimi wajen dakile safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro, Uncategorized

Post navigation

Previous Post: Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
Next Post: Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil Afrika
Yanayin Sanyi Yayi Kamari a Yankin Gaza Tsaro
Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kaduna: Masana Sun Nemi A Sauya Tsohon Wurin Zubar Da Shara Na Tudun-Ilu Afrika
  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
  • Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
  • Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
  • Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.