Zamu tabbatar da kawo karshen hadura a lokacin Bukukuwan karshen shekara – inji Jami’an Hukumar kiyaye hadura a Gombe.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Gombe ta shirya taron fadakar da jama’a game da illar gudu fiye da kima, tare da tukin ganganci yayin bukukuwan karshen shekara.
Kwamandan hukumar kiyaye hadura a jihar Gombe, Mr Samson Kaura ne ya bayyana haka lokacin jawabi ga direbobi da sauran jama’a, yayin gangamin a dakin taro na tashar Dankwanbo Mega Park dake Gombe.
Mr. Kaura, ya tabbatar da cewa ana samun yawan tafiye tafiye a karshen shekara, a saboda haka yabukaci masu ababen hawa da su rika lura tare da bin ka’idojin hanya domin kare rayuwar al’umma.
Ya tabbatar da cewa, ansamu hadura fiye da arba’in da shida a tsakiyar wannan shekarar, kuma mutane sha bakwai sun mutu a jihar Gombe.
A jawaban su, shugaban riko na tashar Dankwanbo Mega Park Malam Sani Sabo da shugaban kungiyar ‘yan achaba a jihar Gombe, Malam Kabiru Jafaru sun bukaci gwamnati da tayi la’akari da gyara hanyoyi da suka lalace a jihar domin gujewa samun hadura.
Malam Sani Sabo da Kabiru Jafaru, sun lissafo hanyar Gombe zuwa Dukku zuwa Darazo, hanyar Gombe zuwa Biu zuwa Maiduguri da hanyar Gombe zuwa Bauchi a matsayin hanyoyi masu muni. Wanda kuma suna haifar da hadura saboda lalacewar su, Inda su kayi fatan gwamnati zata kawo karshen wannan wahalhalu da jama’a ke fuskanta.

A nasu bangaren, daraktar hukumar wayar da kan al’umma jihar Gombe Miss Adalin Waye Patari, shugaban Direbobi na NURTW Malam Musa Yunusa da hakimin Kagarawal Alhaji Usman Ali sun bukaci Direbobi dasu gujewa shaye-shaye a yayin tuki, tare da yawaita gudu fiye da kima.
Inda suka tabbatar da cigaba da fadakar da mambobin su da jama’ar gari domin gujewa samun hadura a fadin kasar nan.


