Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
  • Kannywood: Ali Nuhu Ya Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu Afrika

Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
Published: August 22, 2026 at 8:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jihar Gombe a Arewa Maso Gabashin Najeriya ta yi alfahari tare da maraba da ’yarta, Maryam Ibrahim Dan’azumi, wadda ta zama zakarar gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Makkah Kasar Saudi Arabia.

Maryam ta wakilci Najeriya a rukunin haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, karatu, Tajweed da Tafsiri, inda ta yi galaba a kan mahalarta daga ƙasashe daban-daban, ta zama gwarzuwar gasar ta duniya, tare da ɗaukaka martabar Gombe da Najeriya.

Wannan nasara ta ƙara zama abin tarihi, domin gasar ta bana ita ce karo na farko a cikin shekaru 46 da aka fara bai wa mata damar shiga gasar.

Daga nasarar da ta samu a matakin Ƙaramar Hukumar Gombe, zuwa matakin jiha, sannan ta zama gwarzuwar Najeriya, Maryam ta nuna ƙwazo, jajircewa da ƙwarewa wajen haddar da karatun Alƙur’ani Mai Girma.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya Maryam, iyayenta, malamanta da daukacin al’ummar Musulmi murnar wannan gagarumar nasara, yana mai bayyana ta a matsayin abin alfahari da kuma abin ƙarfafa gwiwa, musamman ga ’yan mata.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
Next Post: Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
  • Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
  • An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika
  • Akwai Yiwuwar Iran Da Amurka Su Cimma Matsayar Dakatar Da Shirin Nukiliya Amurka
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.