Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro Afrika
  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo Afrika
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika

Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya
Published: August 28, 2026 at 10:56 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya ce zai kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya cikin shekara guda da hawansa mulki, idan aka zabe shi a babban zaben shekarar 2027.

Tun bayan fara harkokin siyasa gabanin zaben 2027, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi ta jan hankalin jama’a, musamman kan wasu manufofinsa, ciki har da alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur, lamarin da ya jawo martani daga gwamnati da kuma ‘yan Najeriya.

A wata hira da ya yi da BBC, Atiku ya ce zai dauki matakan da suka dace domin kawo karshen rashin tsaro cikin shekara guda da kafa gwamnatinsa.

Ya ce: “Ba zan dauki fiye da shekara guda ba wajen kawo karshen wannan matsala. Za mu dauki karin jami’an tsaro aiki, sannan mu samar musu da kayan aikin da suka dace.

Haka kuma, za mu samar da isassun kudade domin tallafa wa matasa su kafa sana’o’i da kasuwanci, domin da dama daga cikinsu suna shiga aikata laifuka ne saboda rashin aikin yi. Za mu dauki wadannan matakai, kuma cikin shekara guda za mu kawo karshen rashin tsaro, in Allah ya so.”

Atiku ya kuma ce zai tuntubi shugabannin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, domin farfado da Rundunar Kula da Zaman Lafiya ta ECOMOG, tare da karfafa hadin gwiwar sojojin kasashen yankin wajen yaki da rashin tsaro.

Ya ce Najeriya da Jamhuriyar Nijar suna da dadaddiyar alaka, kuma juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar bai kamata ya zama dalilin lalata dangantakar kasashen biyu ba.

Atiku ya ce: “Za mu tuntubi takwarorinmu da shugabannin ECOWAS, domin na yi imanin cewa idan muka hada kai, za mu iya farfado da ECOMOG tare da samar da kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin dakarun sojin kasashe mambobin kungiyar, ciki har da Côte d’Ivoire, Saliyo da Laberiya, domin tabbatar da zaman lafiya.

“Za mu hada karfi da karfe, mu karfafa hadin gwiwa, sannan mu yi aiki tare domin dawo da zaman lafiya. A yanzu ma sun fi mu ci gaba ta fuskar dimokuradiyya.

“Ban ga dalilin da zai sa Najeriya ta katse dangantakarta da Jamhuriyar Nijar saboda juyin mulkin soja ba. Mene ne ruwanmu da hakan? Najeriya da Nijar kasa daya ce ta fuskar al’umma da tarihi. Mu mutane daya ne. Kasancewar sojoji sun karbe mulki a Nijar bai kamata ya zama dalilin da zai sa Najeriya ta katse alaka da kasar ko kuma ta goyi bayan ci gaba da cire ta daga ECOWAS ba.

“Zan yi kokarin dawo da Nijar, Burkina Faso da Mali cikin ECOWAS, domin mu samu hadin kai. Wannan kuma zai taimaka wajen rage rashin aikin yi a kasashen yankin.”

Da aka tambaye shi ko yana da yakinin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta gudanar da sahihin zabe cikin ’yanci da adalci, Atiku ya nuna shakku kan hakan.

Sai dai ya bukaci ‘yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’unsu, tare da tabbatar da cewa kuri’unsu sun kirga.

Ya ce: “INEC ba za ta yi abin da ya dace ba, domin wannan gwamnati ce ta kawo su. Amma abin da nake son fada wa ‘yan Najeriya shi ne su fito su kada kuri’a. Su tabbatar da cewa kuri’unsu sun kirga, su kare kuri’unsu, sannan su tabbatar da cewa mutumin da suka zaba shi ne wanda za a bayyana a matsayin wanda ya yi nasara.”

Dan takarar ya kara da cewa zaben 2027 zai kasance karo na karshe da zai sake neman shugabancin Najeriya, yana mai cewa idan bai yi nasara ba, zai ci gaba da kasancewa a shirye domin ba matasa ‘yan siyasa shawara.

Da yake magana kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur, Atiku ya ce cire tallafin gaba daya a lokaci guda ba hikima ba ce.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi nazari kan halin da ake ciki tare da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki kafin yanke shawarar da ta dace.

Atiku ya ce: “A cikin shekaru 79 na rayuwata, kuma ina dab da cika shekaru 80, ban taba ganin irin wannan matsanancin yanayin rayuwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta a yanzu ba. Ba na bukatar in tuntubi kowa kafin in yi alkawarin dawo da tallafin, domin na ga halin da al’umma ke ciki.”

Ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cire tallafin man fetur gaba daya a lokaci guda, ta hanyar da ya ce ta jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali, yana mai cewa tasirin matsalar ya tilasta masa barin harkar noma da yake yi.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo
Next Post: Za a Fara Kakar Gasar Firimiya Ta Najeriya, NPFL, 2026/27 Yau Juma’a, 28 Ga Watan Agusta

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’ai A Afirka Sunce Tashin Farashin Mai Kalubale Ne Ga Tattalin Arziki Afrika
‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Najeriya
Kasar Ghana Ta Umarci ‘Yan Kasar Su Daina Zuba Jari A Kasashen Waje Afrika
Harin Iran A Kasar Saudiya Ya Haifar Da Tattaunawa Tsakanin Shugabanni Afrika
Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fiorentina Ta Yi Tayin Farko Ga Manchester United Kan Zirkzee
  • Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro
  • Za a Fara Kakar Gasar Firimiya Ta Najeriya, NPFL, 2026/27 Yau Juma’a, 28 Ga Watan Agusta
  • Atiku: Zaben 2027 Zai Zamo Karo Na Karshe Da Zan Nemi Shugabancin Najeriya
  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
  • Okoye Na Shirin Maye Gurbin Nwabali, AFCON 2025: Wasanni
  • Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Yakin Rasha Da Ukrain Babban Kalubale Ne Ga Kasashen Turai Labarai
  • Jam’iyyar PDP Na Kara Tsunduma Cikin Mawuyacin Hali Shirye-Shirye
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.