Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo
Published: August 27, 2026 at 5:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a Shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun yi kira ga mambobin kungiyar da su kasance masu bin doka da oda, tare da tabbatar da zaman lafiya da sauran al’umma.

Shugabannin sun yi wannan kiran ne yayin wani taro da suka gudanar a jihar Gombe, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi harkokin kiwo, tsaro, zaman lafiya da kuma ci gaban makiyaya a yankin.

Da yake maraba da tawagar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na jihar Gombe, Alhaji Ardo Chindo Abubakar, ya bayyana jin dadinsa da yadda aka zabi jihar Gombe a matsayin wurin gudanar da taron.

Alhaji Ardo Chindo ya kuma yaba da irin kokarin da gwamnatin jihar Gombe ke yi wajen inganta harkokin kiwo da kuma samar da yanayi mai kyau ga makiyaya.

Ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai duba hanyoyin bude hanyoyin shanu, wuraren kiwo da kuma samar da rijiyoyin ruwa domin rage matsalolin da ke tsakanin makiyaya da manoma.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar na kokarin samar da kasuwar shanu ta kasa da kasa a Gombe, wanda ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwancin dabbobi da habaka tattalin arzikin jihar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Nasiru Liman Jalbu, ya gode wa shugabannin jihar Gombe da sauran al’ummar jihar bisa irin kyakkyawar tarbar da aka yi wa tawagar.

Haka kuma, shugaban kungiyar na jihar Borno, Alhaji Musa Maina Harande, ya yaba da yadda aka shirya taron, yana mai cewa tattaunawa tsakanin shugabannin makiyaya na da muhimmanci wajen warware matsalolin da ke addabar harkokin kiwo da zaman lafiya.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka tattauna a yayin taron shi ne batun shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo, wanda shugabannin suka ce ya shafe sama da watanni uku a tsare.

Shugabannin kungiyar sun yi kira ga gwamnonin jihohi da sarakunan gargajiya da su shiga tsakani wajen ganin an saukaka masa tare da samar da hanyar da za a tabbatar da an sake shi.

Sun bayyana cewa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya taka muhimmiyar rawa wajen kokarin samar da zaman lafiya, tare da cewa ya bayar da gudunmawa wajen tallafawa harkokin siyasa da kuma nasarar jam’iyyar APC da zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bayan kammala taron, tawagar ta kai ziyara ga Kwamishinan Ma’aikatar Raya Dabbobi ta Jihar Gombe, Alhaji Salihu Baba Alkali, a ofishinsa.

Da yake jawabi ga tawagar, Kwamishinan ya yaba da irin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa wajen bunkasa harkar kiwo da kuma habaka tattalin arzikin kasa.

Alhaji Salihu Baba Alkali Katukan Nafada ya kuma tabbatar wa shugabannin kungiyar cewa zai sake jaddada kiran da suka yi na neman a saki shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo.

Taron ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyaya, manoma da sauran al’ummomin yankin Arewa maso Gabas.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Mbappé Ya Yi Hat-Trick Yayin Da Real Madrid Ta Lallasa Real Sociedad 4 Da 1

Karin Labarai Masu Alaka

Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya Afrika
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo
  • Mbappé Ya Yi Hat-Trick Yayin Da Real Madrid Ta Lallasa Real Sociedad 4 Da 1
  • UEFA Tana Shirin Janye Barazanar Kauracewa Gasar FIFA
  • Feyenoord Ta Fara Tattaunawa Da Manchester United Kan Daukar Chido Obi Aro 
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
  • Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
  • Sojin Israela Sunkai Hari Kan Falatsinawa Tsaro
  • Iran Zata Kawo Karshen Yaki Da Isra’ila Da Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.