Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, tare da yabawa irin gudunmawar da ya bayar wajen yi wa Jihar Borno da Najeriya hidima.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026, Shugaba Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin amintaccen abokin aiki, ɗan kishin ƙasa kuma mutumin da rayuwarsa ta kasance mai cike da hidima, jajircewa da sadaukarwa.
Ya ce yana taya matar Mataimakin Shugaban Ƙasar, Nana, da ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasarsa murnar wannan muhimmin zagayowar ranar haihuwa.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a lokacin da Shettima yake gwamnan Jihar Borno, da kuma yanzu da yake riƙe da matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya nuna ƙarfin hali, ƙwazo, tausayi da jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma.
Ya kuma yaba da tarihin Shettima a fannin banki, tare da bayyana shi a matsayin mutum mai kishin ci gaban ƙasa da haɗin kan Najeriya.
Tinubu ya ce amincin Shettima ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da goyon bayan da yake bai wa gwamnatin tarayya, da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da nasarar ajandar Renewed Hope sun cancanci yabo.
Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (National Economic Council), Shettima ya samar da jagoranci mai ma’ana wajen daidaita manufofin tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.
Ya ce mutunta kundin tsarin mulki da cibiyoyin dimokuraɗiyya, tare da amfani da tattaunawa da shawarwari wajen tafiyar da al’amura, sun taimaka wajen ƙarfafa shugabanci nagari.
Tinubu ya bayyana hikimar Shettima, amincinsa da kuma fahimtar nauyin da ke kansa a matsayin muhimman abubuwan da suka taimaka wa gwamnatin.
Shugaban ya kuma gode wa Mataimakin nasa bisa irin goyon baya da haɗin gwiwar da yake ci gaba da ba shi wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Renewed Hope da cika alkawuran da aka yi wa ’yan Najeriya.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin gwiwar da ke tsakaninsu zai ci gaba da samar da ci gaba mai ma’ana wajen gina Najeriya mai inganci.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu, a madadin Gwamnatin Tarayya, ya sake taya Shettima murnar cika shekaru 60, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ci gaba da jagorantar sa, Ya kare shi, Ya ƙara masa hikima da lafiya, Ya kuma ba shi tsawon rai domin ci gaba da yi wa Najeriya hidima.


