Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Hadakar Kungiyoyin Sauyin Yanayi Ta Bukaci ‘Yan Siyasa Su Dauki Matakan Kare Muhalli
Published: September 4, 2026 at 10:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hadakar kungiyoyin da ke fafutukar kare muhalli da yaki da sauyin yanayi guda 50 a jihar Kaduna Dake Najeriya ta kaddamar da shirin #Vote4Climate, inda ta fara kai ziyara ga ‘yan takarar siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kungiyoyin na kokarin ganin an mayar da batun sauyin yanayi da kare muhalli cikin muhimman abubuwan da ‘yan siyasa za su sanya a cikin manufofi da kundin alkawurransu na yakin neman zabe.

Gangamin ya zo ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi a Najeriya, inda masu fafutukar kare muhalli ke kira ga ‘yan siyasa da su dauki matsalolin muhalli a matsayin muhimman batutuwan shugabanci, ba wai alkawurran yakin neman zabe na gefe ba.

Da yake magana yayin wata ziyarar neman goyon baya, Shugaban Sadarwa da Dabaru na African Climate Reporters (ACR), wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Kaduna State Climate Change Accountability Mechanism (KADCCAM), Kwamared Ibrahima Yakubu, ya ce hadakar ta fara tattaunawa da shugabannin siyasa, ciki har da Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya.

Yakubu ya ce hadakar ta kunshi kungiyoyi 50 masu zaman kansu da ke aikin kare muhalli, kungiyoyin fararen hula, ‘yan jaridun muhalli, masana ilimin kasa da kuma masana kimiyyar muhalli, wadanda suka hada karfi domin ganin an mayar da yaki da sauyin yanayi cikin muhimman batutuwan zaben 2027.

Ya ce, “Sauyin yanayi ba wata barazana ce da za ta zo nan gaba ba. Tuni yana shafar miliyoyin ‘yan Najeriya ta hanyar ambaliyar ruwa, fari, hamadarawa, sare itatuwa, tsananin zafi, gurbatar muhalli da karancin ruwa.”

A cewarsa, wadannan matsalolin muhalli na ci gaba da yin barazana ga noma, samar da abinci, hanyoyin samun kudin shiga da kuma lafiyar jama’a, abin da ya ce ya sa ya zama wajibi shugabannin siyasa su gabatar da hanyoyin magance matsalolin cikin aikace.

Yakubu ya kara da cewa dubban ‘yan Najeriya sun zama ‘yan gudun hijirar muhalli a wasu al’ummominsu sakamakon lalacewar muhalli, kone-konen daji, sare itatuwa da kuma zaizayar kasa.

Ya bukaci ‘yan takarar siyasa da su sanya takamaiman alkawurra kan sauyin yanayi a cikin manufofinsu, wadanda suka hada da dasa itatuwa, farfado da dazuzzuka, bunkasa makamashi mai tsafta, inganta noma mai dorewa, inganta sarrafa shara, hana ambaliyar ruwa da kuma kare albarkatun ruwa.

Haka kuma, Yakubu ya yi kira ga matasa da sauran masu kada kuri’a da su zabi ‘yan siyasar da suka nuna cikakken kudurin kare muhalli da yaki da sauyin yanayi.

Ya ce shirin #Vote4Climate na da burin mayar da batun sauyin yanayi cikin manyan batutuwan yakin neman zabe a jihohin Najeriya 36, tare da karfafa gwiwar shugabannin da za su zo su samar da manufofi na dogon lokaci da za su kare al’ummomin da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi tare da kara juriyar muhalli.

Kungiyoyin da ke tallafa wa wannan gangami sun hada da Global Climate Youth and Environment, Kaduna Metro-Environmental Initiative da Green Connection, da sauran kungiyoyin fararen hula masu fafutukar ganin ‘yan siyasa sun dauki karin alkawurra kan sauyin yanayi da kare muhalli.

Yakubu ya yi wa dukkan ‘yan siyasa fatan alheri a zaben da ke tafe, inda ya bayyana cewa hadakar za ta ci gaba da ziyartar ‘yan takarar siyasa a fadin Jihar Kaduna, domin neman tabbatar da cewa batun sauyin yanayi da kare muhalli ya samu gurbi a cikin manufofinsu da kundin alkawurran yakin neman zabe.

A nasa bangaren, Sanata Shehu Sani ya yi alkawarin tallafa wa shirye-shiryen kare muhalli da za su taimaka wajen mayar da Kaduna cikin jihar da ta fi korewa tare da dakile matsalolin lalacewar muhalli.

Sanatan ya kuma bukaci matasa da su shiga harkokin dimokuradiyya cikin lumana, su yi amfani da kuri’unsu yadda ya kamata, tare da yin watsi da duk wani nau’i na bangar siyasa a zaben shekarar 2027.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: RSF Ta Nemi A Gaggauta Gano Dan Jarida Moussa Kaka Da Ya Bace A Yamai
Next Post: ACReSAL Ta Tallafa Wa FMC Kumo, Ta Shuka Bishiyoyi Tare Da Gyara Magudanan Ruwa

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin Afrika
‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika
Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya Amurka
An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jam’iyyar APC Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanni a Jihar Neja Labarai
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
  • Iran Tana Duba Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Amurka Afrika
  • Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba” Wasanni
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
  • An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
  • Kasar Botswana Na Samun Kudaden Shiga Da Lu’ulu’u Labarai
  • Afirka Ta Kudu Ta Samu Rigakafin Cutar Boro Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.