Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NEDC Ta Karyata Bada Tallafin Karatun MSc Da Ke Yawo A Kafafen Sadarwa
Published: September 4, 2026 at 1:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya (NEDC) ta musanta wani sako da ke yawo game da wani tallafin karatu na digirin MSc, inda ta bayyana bayanan a matsayin na bogi kuma ba tare da izinin hukumar ba.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce a halin yanzu ba ta karbar neman tallafin karatun MSc da aka bayyana a cikin sakon da ke yawo ba. Sakon ya kuma kunshi wasu sharudda tare da umartar masu neman tallafin da su kai takardunsu ofishin NEDC da ke Polo, Maiduguri.

NEDC ta bukaci jama’a, musamman masu neman tallafin da sauran masu ruwa da tsaki, da su yi watsi da wannan bayanin, tare da kaucewa mika takardun sirri ga wasu mutane ko wuraren da ke ikirarin suna wakiltar hukumar wajen gudanar da wannan shirin.

Hukumar ta yi gargadin musamman kan mika takardu kamar NIN, takardar admission, katin shaida da takardar shedar zama dan asalin wata jiha (Indigene Certificate) ga mutanen da ba su da izini.

NEDC ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan domin kauce wa fadawa cikin shirye-shiryen damfara da kuma amfani da sunan hukumar ba tare da izini ba.

Hukumar ta shawarci jama’ar da ke son samun sahihan bayanai kan shirye-shiryenta, ayyukan tallafi da sauran damarmaki da su rika dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma na NEDC da kuma sanarwar da hukumar ta tabbatar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: ACReSAL Ta Tallafa Wa FMC Kumo, Ta Shuka Bishiyoyi Tare Da Gyara Magudanan Ruwa
Next Post: Borno: An Yi Kwanton Bauna Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna

Karin Labarai Masu Alaka

Kotun Daukaka Kara A Faransa Zata Tabbatar Da Hukuncin ‘Yan Jam’iyyar Ra’ayin Rikau Labarai
Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Haramtawa Amurkawa Shiga Kasashen Afrika
Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
Mutane Biyu Sun Mutu A Yayin Zaben Shugabannin Gundumomin APC A Jihar Ondo Najeriya
Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
  • Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
  • Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
  • Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
  • Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
  • Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli Afrika
  • Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.